Boko Haram ta shafe shekara 14 tana tayar da ƙayar baya a yankin da nufin ƙaddamar da daular Musulunci. Photo: AFP

Aƙalla manoman shinkafa 15 aka kashe, sannan ana fargabar an sace wasu da dama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, sakamakon hare-hare uku da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wasu ƙauyuka uku, a cewar wani shugaban manoma na yankin a ranar Litinin.

Sakataren kungiyar manoman shinkafa ta Zabarmari, Mohammed Haruna, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa harin ya faru ne a ƙauyukan Koshebe da Karkut da Bulabulin da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar, wanda ke da nisan kilomita 15 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Borno bai amsa bukatar Reuters ta neman jin ta bakinsu ba game da harin, wanda ya faru a ranar Lahadi.

Haruna ya ce mayaƙan ƙungiyar sun mamaye ƙauyukan ne a kan babura inda suka far wa manoman da suke girbin amfanin gona a gonakinsu na shinkafa.

"Ba su yi amfani da bindiga wajen kashe ba, da adduna da wuƙaƙae suka yi amfani wajen hallaka wasu, yayin da suka fille wa sauran kawuna," in ji Haruna.

Ya ce an tabbatar da mutuwar manoma 15 a a harin, ina ya ƙara da cewa da ƙyar sauran suka tsallake rijiya da baya. Har yanzu ba a san yawan waɗanda ba a ji ɗuriyarsu ba.

Harin yana daga cikin jerin na baya-bayan nan da ƙungiyar Boko Haram ta kai a arewa maso gabashin Nijeriya. Ƙungiyar ta shafe shekara 14 tana tayar da ƙayar baya a yankin da nufin ƙaddamar da daular Musulunci.

Aƙalla mutum 40 aka kashe a makon da ya wuce a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya, wanda shi ne babban hari na farko da ƙungiyar ta kai jihar a cikin wata 18 ɗin da suka wuce.

Kazalika a makon jiya wata rundunar haɗin gwiwa ta sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS a Nijeriyar suka yi nasarar daƙile wani yunƙurin kai hari da masu tayar da ƙayar baya da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka yi a Jihar Kano.

A baya-bayan nan Shugaba Bola Tinubu da majalisar ministocinsa suka amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudi na dala biliyan 2.8 don ayyukan gaggawa da suka haɗa da na tsaro da fannin soji.

Tinubu, wanda batun taɓarɓarewar tattalin arziki ya sha masa kai a yanzu, har yanzu bai ce komai ba a kan yadda zai magance matsalar rashin tsaro a wasu sassan arewacin ƙasar.

Reuters