‘Yan bindiga sun sace mutum takwas a wani hari da suka kai a karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna a arewacin Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a kauyen Dan Honu.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar ta Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ta ce tana gudanar da bincike.
Wani mazaunin kauyen, Mohammed Danjuma, wanda ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutum goma sha shida aka yi garkuwa da su amma mutum takwas sun kubuta.
"A yayin da suke kokarin yin amfani da karfi don shiga gidana, daya daga cikin ‘yan bijilanti da ke unguwarmu ya harba bindiga, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka tafi," in ji shi.
Shi ma Malam Suleiman, wanda aka yi garkuwa da shi amma ya tsere, ya ce ‘yan bindigar sun tafi da ‘ya’yansa biyu.
Kakakin rundunar Mansur Hassan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa lamarin ya faru ne ranar Talata amma ba su samu labari ba sai yau Alhamis.
Ya ce sun dukufa wurin ganin sun kubutar da mutanen, sannan suna gudanar da bincike.
Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a wasu yankuna na arewacin Nijeriya inda barayin kan tare hanya ko su shiga gonaki da makarantu suna sace mutane.