Akalla mutum 30 ne ake fargabar an yi garkuwa da su, ciki har da dalibai a Arewacin Kamaru.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutanen da aka sace sun fito ne daga kasar Chadi mai makwaftaka kamar yadda Magajin Garin Touboro ya bayyana a ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da daddare, kamar yadda Magajin Gari Celestin Yandal ya ce.
Wata majiya daga bangaren tsaron Kamaru ta tabbatar da faruwar lamarin ba tare da bayar da bayanai kan yadda lamarin ya faru ba, inda ta ce tana zargi an yi garkuwa da su ne domin karbar kudin fansa wanda ba sabon abu ba ne a yankin.
Majiyar ta ce ba a tabbatar da ko su wane ne wadanda aka sace ba amma mai yiwuwa akwai dalibai ‘yan Chadi daga cikinsu.
Dalibai daga Chadi na bin hanyar Touboro domin zuwa birnin Ngaoundere don yin karatun jami’a.
Kamaru na fuskantar matsaloli da dama na tsaro wadanda suka hada da na Boko Haram a Arewa mai nisa da kuma rikicin ‘yan a-ware a yankin renon Ingilishi.