'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Nijeriya akalla 26 sannan suka jikkata takwas a wani harin kwanton-bauna da suka kai musu a tsakiyar kasar.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi da maraice, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu majiyoyi biyu suna shaida masa.
Haka kuma, kakakin rundunar sojin sama ta kasar ya ce wani helikwafta da ke aikin ceto dakarun da suka jikkata ya yi hatsari ranar Litinin da safe a yankin, inda sojoji ke fafatawa da 'yan bindiga, ba tare ya bayyana cewa matukin jirgin da fasinjojin da ke cikinsa sun tsira ba.
Majiyoyin sojoji biyu ba sa so a ambaci sunayensu saboda ba a ba su damar yin magana ba sannan rundunar sojin ba ta ce komai kan batun ba.
"Sojojinmu guda 23 sun mutu, cikinsu har da manyan sojoji uku, da 'yan bijilante na JTF guda uku yayin da sojoji takwas suka jikkata a fafatawa mai zafi da aka yi a babban titin Zungeru zuwa Tegina," a cewar majiya ta farko.
Majiya ta biyu ta tabbatar da mutuwar adadin mutanen da majiya ta farko ta bayyana amma ta ce 'yan bindigar sun fuskanci "gagarumar asara".
Ta kara da cewa sun rasa hanyar magana da helikwaftan rundunar sojin kasar da aka tura wurinsu bayan ya kwashe gawa 11 da wadanda suka jikkata bakwai.
A cewarta, helikwaftan ya yi hatsari ne sakamakon harbin da 'yan bindiga suka yi masa.
Kakakin rundunar sojin sama ta Nijeriya ya tabbatar da cewa helikwafta mai lamba Mi-171 ya yi hatsari yayin da yake "aikin kwaso mutanen da hatsari ya hada da su" ranar Litinin bayan ya tashi daga Zungeru.
"Jirgin ya tashi daga Makarantar Firamare ta Zungeru a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna amma daga bisani aka gano ya fadi a kusa da kauyen Chukuba na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja," a cewar sanarwar da kakakin rundunar sojin saman Edward Gabkwet ya fitar.
Ya kara da cewa an soma yunkurin ceto wadanda suke cikin jirgin kuma an kaddamar da bincike kan lamarin.