Rahotanni daga Jihar Kwara da ke arewacin Nijeriya na cewa hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 150 a Jihar.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin a lokacin da kwale-kwalen ke jigilar mutane kusan 300 da suka halarci wani bikin aure. Sai dai batun bai fito ba sai yau Talata.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta Kwara ta fitar ta ce kwale-kwalen na dauke da mutanen da suka fito daga garin Egboti na jihar Neja kan hanyarsu ta zuwa karamar Hukumar Patigi a jihar Kwara.
Sanarwar, wadda ta ambato Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq yana ta'aziyya ga iyalin mutanen da lamarin ya shafa, ta kara da cewa mutanen 'yan asalin karamar hukumar ta Patigi ne.
Tun da farko Jaridar Tribune a Nijeriya ta ruwaito cewa akalla gawarwaki 50 aka gano a yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen.
Rahotanni sun ce igiyar ruwa ce ta kwashi kwale-kwalen ta buga shi da bishiya da ke cikin kogin.
Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Nijeriya kuma ko a kwanakin baya sai da sama mutum 30 suka rasu sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihar Kano da ke arewacin kasar.