Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afka cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na dare inda suka shafe sama da awa uku suna harbe-harbe. / Hoto: AA

Aƙalla mutum bakwai aka kashe a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Mai Dabino da ke Ƙaramar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar wa TRT Afrika da faruwar lamarin.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da mutanen da ba a san iyakarsu ba waɗanda akasarinsu yara ne da mata.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afka cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na dare inda suka shafe sama da awa uku suna harbe-harbe.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa bayan maharan sun kashe mutanen, sannan suka cinna musu wuta.

Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa kafar watsa labarai ta Channels a Nijeriya cewa maharan sun je garin da muggan makamai inda suka ƙona gidaje da dama da shaguna da motoci na miliyoyin nairori.

Ko a watan Mayun da ya gabata sai da ‘yan bindigan suka kai makamancin wannan harin a ƙauyen ‘Yar-Malamai da ke Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina inda suka sace sama da mutum 80.

Haka kuma a watan nan na Yuni ‘yan bindigar sun kai hari a wasu ƙauyuka biyu da ke karamar hukumar Kankara ta Katsina inda suka kashe mutum 26 daga ciki har da 'yan sanda.

TRT Afrika da abokan hulda