An lalata akalla gidajen tarihi hudu a Yammacin yankin Darfur ciki har da fitaccen gidan tarihin nan na Nyala Museum. / Hoto: Sudan National Museum

Daga Dayo Yussuf

Shahararren marubucin Birtaniya George Orwell ya ce "babbar hanyar rusa mutane ita ce ka lalata fahimtarsu kan tarihinsu".

Labaran kai hare-hare ba kaukautawa da harbe-harben bindiga da hayaki da ke fitowa daga gine-gine a babban birnin Sudan, Khartoum, abubuwa ne da ke sanya tsoro a zuciyar Agnes Kinyua, in ji wata malamar jami'a da ke koyarwa a fannin tarihi a Jami'ar Strathmore a kasar Kenya.

Yayin da take bibiyar yakin basasa a kasar Afirkan, babban abin da ke ba ta tsoro shi ne tarihi – littattafai da kayan tarihi da kuma gaba daya gidajen tarihi – sun kasance wadanda yaki yake shafa.

"Na sanya ido ga wadanda suke yakin. Ba sa damuwa idan suka kona littattafai. Suna kona komai ne, suna sata kuma suna lalata abubuwa.

Bayan kayan tarihi, muna da wurare masu tarihi a Sudan. Abin ya dame ni, kuma na san duk wani da ya damu da tarihi shi ma haka yake ji," in ji Agnes.

Yayin da babu wata alama da ke nuna karshen yakin, za a iya cewa damuwar da mutane suke tana da tushe.

Kungiyar Heritage for Peace ta ce akalla wuraren al'adu da tarihi 28 ne aka hara a kasar. Hoto: Sudan National Museum

"Da zarar kayan tarihinmu sun kare, ba za mu iya samun sahihan bayanai ba. Babu sauran tarihi," kamar yadda Agnes ta shaida wa TRT Afrika.

Asarar da yaki ke jawowa

Yaki, musamman na cikin kasa yana daya daga cikin abin da ke dagulawa da lalata abubuwa. Abu ne da ke sa kowa yake neman tsira.

Akwai bayanai da ke cewa wasu na amfani da mutane a matsayin garkuwa yayin yaki. Kayayyakin tarihi ciki har da gumaka wadanda suke nuna yadda kasa ko al'umma suka samu ci gaba suna cikin abubuwan da yakin ya fi shafa.

"Yana da kyau a fahimci muhimmancin kayan tarihi. Bai kamata ka lalata kayan tarihi ba saboda huce fushinka kan daya bangaren da kake yaka ba," in ji Agnes.

Tun lokacin da aka fara yaki a Sudan a tsakiyar watan Afrilu, rahotanni da suka fito daga Khartoum sun ce an kona tarin takardu da littattafai.

Ana tsoron kayan tarihi da suka kai shekara 1070 kafin zuwan Annabi Isa (AS) suna cikin hadarin za a kona su a Sudan. Hoto: Sudan National Museum

Wani rahoton Heritage for Peace wato wata kungiya mai zaman kanta da ke adana kayan tarihi a Sudan, ta ce a tsakiyar watan Afrilu Hukumar Gidajen Tarihi a Khartoum tana da tarin kayayyaki da aka kona.

"Gidan tarihin wanda wani bangare ne na Jami'ar Khartoum, yana da wasu tsirrai da ba a saba ganin irinsu ba, da wasu jinsi da suke barazanar bacewa a Sudan, da dabbobi da kwari (akalla jinsi 100)," in ji rahoton.

"Abin takaicin an lalata wannan fanni, kuma ginin kansa an lalata shi."

Gidan tarihin wanda yake tsakiyar birnin Khartoum yana bangaren sojojin Sudan ne, kuma wuri ne da aka hana fararen hula shiga.

Duka bangarorin biyu da ke yaki da juna suna zargin daya bangaren da alhakin lalata muhimman kayan tarihin.

Rundunar Rapid Support Forces (RSF), wacce take yaki da sojoji, ta yada wani bidiyo a watan Yuni, inda a cikinsa ake nuna wasu akwatuna da suke dauke da kayan tarihi da sauran muhimman abubuwan tarihi.

Masana masu tono kayan tarihi a Sudan sun ce suna kokarin adana kayayyakin da za su iya tun bayan da yaki ya barke. Hoto: Sudan National Museum

Rundunar RSF ta yi watsi da rahotanni da ke cewa mambobinta sun lalata wasu muhimman kaya da wuraren tarihi, inda ta bayyana hakan da "ba gaskiya ba ne kuma labari ne marar tushe."

Ko ma mene ne gaskiyar batun dangane da wanda ya kamata a dora wa alhakin abin, muhimman abu shi ne an riga an lalata hujjojin tarihi.

Mutane kamar Agnes suna damuwa idan aka zuba ido ba a yi komai ba kan al'amarin, Sudan ce za ta yi asara sosai.

Kungiyar Heritage for Peace ta ce akalla wuraren al'adu da tarihi 28 aka hara a kasar ko kuma aka lalata su.

Matsayin Sudan a tarihi

Sudan tana da muhimmanci ta fuskar dadadden ci gaban yankin Gabashi da Arewacin Afirka.

Daga tsakiyar kasar inda kogin Nilu biyu suka hadu – Kogin Nilu Shudi (Blue Nile) da Kogin Nilu Fari (White Nile) – akwai Masarautar Kush wacce ta yi suna wajen kasuwanci da zinare da karfe. Kuma ita ce babbar hanya tsakanin masarautun arewaci da kudancin Sahara.

Tsibirin Meroe da Tsibirin Barkal muhimman wuraren tarihi ne da Hukumar Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta san da zamansu. / Hoto: Sudan National Museum

Akwai dalar hubbare wadanda suke nuni ga yadda yankin ya yi alaka da makwabtansu daga arewa, wato kasar Masar.

Gaba daya wadannan abubuwan tarihin da suka wanzu tun shekarar 1070 kafin zuwan Annabi Isa suna cikin barazanar kona su, idan ba a yi tsayuwar daka wajen kare su ba yayin da ake ci gaba da barin wuta a Sudan.

"Wannan ana maganar Sudan ne kadai," in ji Agnes. "Idan ana rikici ko yaki galibi mutane suna mantawa ne da gidajen tarihi."

Somaliya kasa mai tarihi da al'adu sosai, ita wata misali ce a cikin nahiyar.

"An yi asarar yawancin kayayyakin tarihin kasar saboda shekarun da aka kwashe ana yaki. Yanzu, muna kokarin samar da alaka tsakanin tarihi da al'adar yankin, don mu alkinta su saboda 'yan baya.

"Kada mu bari abin da ya faru a Somaliya ya faru a Sudan, ko kuma a Yammacin Afirka," in ji Agnes.

"Ya kamata masu raji su kare kayan tarihi. Yayin da suke gudun neman tsira da iyalansu, ya dace su gudu tare da wadannan muhimman kayan tarihi, idan za su iya," a cewar Agnes.

Tun lokacin da aka fara yaki a Sudan a tsakiyar watan Afrilu, an lalata takardun tarihi. Hoto: Sudan National Museum

Masana masu tono kayan tarihi a Sudan sun ce suna kokarin kare kayan tun bayan da yaki ya barke.

"Muna bakin kokarinmu don tabbatar da cewa kayan tarihin suna nan babu abin da ya shafe su. Muna so mu tabbatar cewa kowa ya san su," in ji Ibrahim Musa, Darakta Janar na Hukumar Gidan Tarihin Sudan.

Agnes ta ce ya kamata a sanya batun kula da kayan tarihi cikin aikin masu kiyaye zaman lafiya.

"Majalisar Dinkin Duniya za ta shiga batun. Saboda sauran hukumomi da suke da iko kamar Tarayyar Afirka da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) su ma za su iya biyo sahu.

Za su iya taimaka wa wajen samar da tsaro ko kuma taimaka wa wajen kai wadannan kayayyakin tarihin zuwa wajen da ba shi da hadari," in ji ta.

Kamar yadda Kungiyar Heritage for Peace ta ce akalla gidajen tarihi hudu a yankin Yammacin Darfur aka lalata ciki har da fitaccen gidan tarihin Nyala Museum, wanda aka lalata rufinsa, abin da zai iya sa ruwan sama ya yi masa barna.

Masana sun bukaci a shigar da adana kayan tarihi cikin aikin kiyaye zaman lafiya. Hoto: Sudan National Museum

Sudan tana da manyan gidajen tarihi akalla shida da kuma wasu kanana da suke warwatse a kasar.

Hukumar Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta san da zaman wurare biyu a Sudan a matsayin muhimman Wuraren Tarihi na Duniya.

Wuraren su ne: Tsibirin Meroe wanda yake da dalar tsofaffin hubbare mafiya girma a Afirka da tsaunin Jebel Barkal wanda ke kusa da hubbaren da wasu muhimman wurare a kusa da kogin Nilu.

Kowane lokaci aka tayar da bam kuma gini ya lalace yayin wannan yaki, ran Agnes yana baci matuka.

TRT Afrika