Daga Abdulwasiu Hassan
Jagoran rundunar sojin kasar Sudan (SAF) Janar Abdel Fattah al-Burhan ya fara ziyara a kasashe kamar Masar da Sudan ta Kudu da Qatar da kuma Eritriya.
Tafiye-tafiyen diflomasiyya a yayin da kasarsa Sudan take cikin yaki ya nuna sauyin salo daga bangaren al-Burhan, wanda har zuwa karshen watan Agusta ya ki barin hedkwatar rundunar sojin kasar da ke birnin Khartoum.
"Dakarun sojin sun bai wa 'yan Sudan da kuma duniya baki daya tabbaci cewa za su kammala shirin mika mulki a hannun farar hula bayan samun nasara a kan 'yan tawaye," kamar yadda aka ruwaito al-Burhan yana cewa a birnin Doha.
Ya ci gaba da rike wannan matsayi lokacin da ya kai ziyara kasar Masar da kuma Sudan ta Kudu da Eritriya daga baya. Jagoran sojojin Sudan din ya kai ziyara Turkiyya, wato wata kasa da take da alaka mai kyau da Sudan a tsawon shekaru.
A ziyarar da ya kai a baya-bayan nan, Al-Burhan ya gana da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba.
Ana sa ran janar din wanda ya ayyana rundunar Rapid Support Forces (RSF) da haramtacciya, zai kai ziyara Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kafin halartar Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.
Dalili da tasiri
Mene ne abin da ya sa al-Burhan yake ziyarce-ziyarcen diflomasiyya? Khalid Omer Yousif na jam'iyyar Sudanese Congress Party (SCP) ya ce Burhan yana ziyarce-ziyarce ne don ya karfafa ikonsa.
"Ina ganin yana so ne ya karfafa karfin sojojinsa a yakin da ake yi ta hanyar yin magana da kasashe makwabta da sauran manyan kasashen duniya wadanda za su iya yin tasiri a halin da ake ciki a Sudan," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Yousif ya ce har sai bayan 'yan makonni da suka wuce, kasancewarsa a hedikwatar sojoji a birnin Khartoum ya "takaita ikonsa na hulda da manyan masu fada a ji a duniya" yana kokarin kulla hulda ne.
"Ina ganin yana so ne ya karbe iko na wakiltar kasar Sudan. Hakan yana cikin dalilan da suka jawo rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF."
Ba mataimakin shugaban jam'iyyar SCP kadai ne yake kallon matsayin da al-Burhan ya dauka a matsayin wata dabara ta kulla kyakkyawar dangantaka da kasashen duniya ba.
Kholood Khair, darakta kuma wanda ya kafa cibiyar nazari ta Confluence Advisory, shi ma ya yi amannar cewa jagoran sojojin kasar yana kokarin amfani da diflomasiyya ne wajen cimma burinsa.
"Ko ba domin komai ba, a birnin Cairo ne ko a Sudan ta Kudu ne, ya kan sanya kot madadin kakinsa na soji. Yana kokarin samun halarci a matsayin wakilin Sudan a tsakanin kassshen duniya," kamar yadda Khair ya shaida wa TRT Afrika.
Ko za a iya cewa al-Burhan yana cikin zakuwa ko kuma a ce mutum ne da ya sanya wani aiki a gabansa hakan ya danganta ne kan wanda ka tambaya.
"Ina tunanin shi mutum ne da yake kokarin samar wa sojojin goyon baya don taimakawa wajen kawo karshen yaki da RSF," in ji Cameron Hudson wani tsohon jami'in diflomasiyya na Amurka.
"Kasar ta zaku, shi bai zaku ba. Kasar ta zaku a kawo karshen wannan rikici saboda yana jawo asara a kowace rana," in ji Cameron. "Ina ganin al-Burhan yana kokarin samar wa sojojin kasar goyon baya ne don kawo karshen rikicin. Ni hakan nake fassara aikace-aikacensa."
Tasirin diflomasiyya
Ba za a iya ganewa ko tafiye-tafiyen al-Burhan sun fara yin tasiri ba, amma bakin masana ya zo daya kan cewa yana so a rika kallonsa a matsayin jagoran Sudan maimakon jagoran RSF Mohamed Hamdan Daglo.
"Tsawon shekaru kasashe kamar Qatar sun taimaka wa gwamnatin al-Bashir ta bangaren kudi da kuma siyasa, kuma al-Burhan da magoya bayansa na son samun wannan goyon baya," in ji Khair.
"Ba mu ga yiwuwar haka ba daga bangaren Qatar kan cewa za su bayar da goyon baya kamar yadda suka yi a baya, amma al-Burhan zai so ya rika gabatar da kansa a matsayin halartaccen jagoran Sudan."
Cameron ya ce al-Burhan zai yi iya kokarinsa wajen neman kasashen da ke goyon bayan Hamdan su dawo bangarensa.
"Kuma zai bukace su da su daina bai wa dakarun RSF gudunmawar soji. Mun san cewa UAE tana taimaka wa RSF ba kai-tsaye ba. Ina tsammanin idan ya je can, zai ce musu su sake tunani," in ji Cameron.
"Ban san ko zai samu goyon bayan wadannan kasashen ba. Amma na san abin da zai nuna musu shi ne yana da gogewar yin nasara a yakin, kuma zai iya tafiyar da al'amura don kare manufofinsu.
"Idan suka yarda da shi, to zai kara karfafa musu gwiwa kan cewa amincewa da shi, zai sa a iya samun nasara kan abin da ya sanya a gaba."
Da wuya samun zaman lafiya a nan kusa
Yakin da aka fara a Sudan a watan Afrilu bai tsaya kawai kan asarar rayuka da barnar dukiya ba. An kashe fiye da mutum 4,000 kuma wasu miliyoyi ne aka raba da muhallinsu yayin da ake ci gaba da yin biris da kiraye-kirayen tsagaita wuta.
Akwai mahanga biyu dangane da yadda za a kawo karshen rikicin, amma bakin masana ya zo daya kan cewa Sudan tana bukatar komawa kan tsarin dimokuradiyya.
"Ina ganin mafita daya ce kawai ita ce a rusa rundunar RSF kuma ka da su kara dawowa. Ina ganin Sudan a ko da yaushe tana da sojoji. Ya kamata su yi nasara, kuma daga nan sai su koma bariki kuma sai gwamnatin farar hula ta mulki kasar," kamar yadda Cameron ya shaida wa TRT Afrika.
Dangane da halin da ake ciki, yawancin masana ba sa ganin za a iya samun nasara a fagen daga. Sun yi amannar cewa akwai bukatar tattaunawa kafin a kawo karshen yakin.
"Adadin mutanen da suke mutuwa yana karuwa a kullum. Yanzu duniya ta fara fahimtar cewa yaki ba shi da amfani sam, ko cewa wani bangare zai yi nasara kuma yakin zai zo karshe," in ji Khair.
"Duka bangarorin biyu suna kokarin fara harkokin siyasa saboda da zarar an fara tattaunawa za su iya kafa gwamnati don rike karfin ikonsu a siyasance."
Yousif yana ganin cewa ba za a iya samun hanyar warware yakin Sudan ta fuskar amfani da karfin soji ba.
"Tattaunawa ita ce hanya daya tilo ta warware matsalar. Muna kan hanyar shiga wata biyar da fara yaki. Abin babu kyau sam, kuma a fili yake kowa zai iya gani," in ji shi.
"Mutanen Sudan da dama ne aka raba da muhallinsu. Dubbai ne aka kashe ko aka jikkata. Yanzu kasar tana kan hanyar fuskar masifar yunwa."
Yayin da ake tattaunawa kan abin da zai faru, wake goyon bayan wancan bangaren, 'yan Sudan da ke cikin wahala suna jiran jin abin da suke addu'a a kai: wato duka bangarorin biyu su fahimci rashin amfanin yakin.