Bayan shafe sama da makwanni biyu ana ba-ta-kashi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF kan wani birni mai muhimmanci a yammacin Darfur ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 123 , kamar adda wata ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa ta sanar a ranar Lahadi.
Yaƙin da ake yi a birnin el-Fasher, wanda shi ne babban birnin lardin Arewacin Darfur, ya yi sanadin sama da mutum 930 sun jikkata, kamar yadda ƙungiyar Doctors without Borders ta sanar.
"Wannan wata alama ce ta ƙaruwar rikici," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.
"Muna kira ga ɓangarorin masu rikici da juna kan su mayar da hankali domin bayar da kariya ga farar hula.
Fiye da mutane 14,000 aka kashe a Sudan
Rikici tsakanin sojoji da dakarun RSF ya ƙara ƙamari a farkon watan nan a birnin, wanda ya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Birnin El-Fasher ya zama cibiyar rikici tsakanin sojoji da RSF. Birnin dai shi ne wuri na ƙarshe mai ƙarfi da har yanzu sojoji ke rike da shi a yankin na Darfur.
Rikicin Sudan ya faro ne a watan Afrilun bara lokacin da rikici ya barke tsakanin shugabannin sojoji da na RSF a babban birnin kasar, Khartoum, da sauran wurare a kasar.
Rikicin ya kashe mutane fiye da 14,000 tare da raunata wasu dubbai a yayin da ake samun rahotannin cin zarafi da cin zarafi da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce sun kai laifukan yaki da cin zarafin bil adama.
Yunwa
Hakan kuma ya jefa al'ummar kasar cikin halin yunwa. Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi bangarorin da ke gaba da juna a farkon wannan wata cewa, akwai matukar hadarin yunwa da mutuwa a yankin Darfur da sauran wurare a kasar Sudan idan ba su bar agajin jin kai a yankin yammacin kasar ya shiga ba.
Rundunar RSF ta kafa runduna a cikin 'yan watannin da suka gabata don neman kwace ikon el-Fasher. Dakarun RSF sun yi wa birnin kawanya tare da kaddamar da wani gagarumin hari a yankunan kudanci da gabashin kasar a farkon wannan wata.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, fadan ya sake barkewa a ranar Alhamis a sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da ke unguwar Salam a yankin arewacin birnin, da kuma yankunan kudu maso yammacin kasar.