Shugabannin al'umma sun hada hannu domin jan hankalin matasa daga shiga rikici a Momasa. Hoto/TRT Afrika

Naim Sultan ya shiga matsaloli da dama kuma ya fita daga cikinsu. Tun daga kan damuwa da tu’ammali da miyagun kwayoyi da daina zuwa makaranta da tunanin kashe kai.

Ya kasance yaro mai zuwa makaranta a kullum a Mombasa a lokacin da ya rasa mahaifiyarsa a 2017.

Wannan ne lamarin da ya sa ya soma shiga matsala – wanda kaduwar da ya yi kan hakan ta sa ya soma shiga wani hali, inda har ya kusan shiga wata kungiya ta masu aikata laifi.

Daga nan ne Babu Ali ya shigo, wanda shi ne shugaban gudanarwar Masallacin Mandhry kuma wanda ya kirkiro shirin bayar da shawarwari na Mandhry mentorship programme ga matasa a tsohon garin Mombasa.

Sai ya dauki Naim, a lokacin yana cikin rudani, inda ya mayar da shi makaranta. A hankali aka rinka samun ci gaba.

Bayan shafe shekaru ana ba shi shawarwari da kuma sa shi motsa jiki da sauran abubuwan yau da kullum, sai Naim ya sauya. Ba wai kawai ya kammala jami’a ba, amma ya zama dan kasuwar da ya yi nasara a Kenya.

Matasan da aka yi asara

Labarin Naim labari ne mai ratsa zuciya. Akwai dubban matasa irinsa, inda wasu ba su wuce shekara goma ba ma amma suna fama da irin wannan matsalar a Mombasa, inda suke sauka daga kan layi.

Rashin aikin yi da shaye-shaye da rashin lafiyar kwakwalwa na daga cikin manyan matsalolin da matasa ke fuskanta a birni na biyu mafi girma da ke Kenya.

Wasu daga cikinsu kan daina zuwa makaranta, su shiga shan miyagun kwayoyi, tare da shiga gungun masu aikata laifi inda suke addabar mazauna wurare kamar Kisauni da Likoni da Old Town.

Kadan daga cikinsu ma na zama kungiyoyin da ke dauke da makamai. “Matasa da dama da ke Old Town na saurin karaya inda suke fadawa cikin muganyar dabi’a,” kamar yadda Babu Ali ya shaida wa TRT Afrika.

Gyara kuskure

Shekaru 15 da suka gabata, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a asibitin Mandhry ya lura da cewa wani lamari na tafiya ba daidai ba. Wani rukuni daga cikin masu wa’azi da likitoci da shugabannin al’umma da ‘yan kasuwa sai suka hada hannu inda a duk ranar Juma’a da dare suke bayar da shawarwari inda suke bayar da karfin gwiwa ga matasa da su guje wa abubuwa marasa kyau da kuma ci gaba da karatu.

Wasu daga cikin matasan Mombasa sun fada rayuwar shaye-shaye, sai dai a yanzu hakan ya zama tarihi. Hoto/TRT Afrika

Mun soma da yara bakwai zuwa takwas. Daga nan ne ajin ya soma habaka har aka kai 25. Sai aka soma bayar da labari a cikin unguwa, a cikin watanni, sama da yara 100 sai suka soma neman gurbin shiga.

Taron da ake yi na bayar da kwarin gwiwar sai ya zama ya yi fice inda har aka rasa wurin zama a masallaci,” kamar yadda Babu Ali ya shaida. Hanyar da aka rinka amfani da ita wurin bayar da kwarin gwiwa ga matasan Kenya da dama wato ta hanyar shirin bayar da shawarwari, a halin yanzu an soma yin wannan shiri a masallatai da coci-coci da wasu daga cikin gidan marayu har ma da wasu makarantu a Mombasa.

An mayar da hankali musamman wurin wasannin motsa jiki domin sa matasan su zama suna yin wani abu don kada su shiga hanyar da ba daidai ba.

A coci-coci, malaman coci na wa’azi tare da hadin gwiwar masana halayyar dan adam da shugabannin matasa musamman lokutan hutun makaranta.

“Duk bayan watanni uku, muna magana ga wadannan matasan kuma ta hanyar wadannan shirye-shiryen, muna sanin irin kalubalen da matasan ke fuskanta – musamman tu’ammali da miyagun kwayoyi da rashin aikin yi,” in ji Lameck Onoka, wani jagoran matasan Kiristoci kuma malamin makaranta, a tattaunawarsa da TRT Afrika.

“A baya, ba su da masu ba su shawarwari masu kyau. A yanzu, da alama sun samu kwarin gwiwa domin gyara rayuwarsu: wasu daga cikinsu sun samu taimako a addini, wasu kuma sun koma yadda suke inda suka yi aure.”

Matsalolin da ake fama da su

Tafiyar ba ta kasance mai dadi ba. Ba duka matasa ne ke da sha’awar shirye-shiryen gyaran hali ba.

“A cikin shekaru masu ban sha'awa, idan an danganta ku da abokai marasa kyau, za su kai ku su baro," in ji Immaculate Kyeo, dalibin injiniya a Jami'ar Fasaha ta Mombasa.

“An ta kokarin shawo kaina domin shiga shirye-shiryen bayar da shawarwari na coci, zuwa yanzu na fahimci kaina – abin da nake da karfi a kai da rauni – da kuma samun salama a zuciyata. Haka kuma na yi kokarin haduwa da mutane wadanda suka taimaki ni yadda ya kamata,” in ji shi.

Karancin kudi da ake fama da shi lokaci zuwa lokaci kalubale ne sai dai ba ya hana su aikin da suke yi.

Kokarin hadin gwiwa

Jami’o’i daban-daban da makarantu a Mombasa a halin yanzu suna gudanar da ayyukan bayar da shawarwari kan irin aikin da mutum ke son yi.

Malaman makaranta da masana halayyar dan adam da ma’aikata da ‘yan jarida da ‘yan kasuwa sun soma kai ziyara irin wadannan cibiyoyin a wannan watan na Maris domin bayar da shawarwari ga dalibai kan yadda za su yi karatu da kuma muhimmancin lafiyar kwakwalwa.

Babban dalilin yin hakan shi ne kawar da hankalinsu daga miyagun kwayoyi da kuma shirya su don samun makoma mai kyau.

“Na kasance malama a makarantar Alidina Visram Boys’ High School. Sai na ga alamar cewa dalibaina na bukatar shawarwari sakamakon suna fuskantar kalubale a makaranta da kuma matsalar kudi a gida, wanda hakan ya sa suke shiga wani hali har su gaza samun sakamako mai kyau a makaranta,” in ji Elye Abdul Halim, wadda a yanzu ita ce shugabar makarantar Eman Girls da ke Mombasa a tattaunawarta da TRT Afrika.

Sakamakon na nan domin kowa ya gani. Bayan tattaunawa mai kyau da malamai, Halim ta gano gagarumin sauyi a ɗabi'a da tarbiyyar ɗalibai. Sakamakon karatunsu ya inganta, haka nan basirarsu ta kara kaifi.

Dangantaka tsakanin su da malamansu ta kara karfi. Yayin da matasan Mombasa ke jin daɗin aikinsu, ba su waiwayawa baya.

Irin su Halim sun himmatu fiye da kowane lokaci, don ci gaba da aiwatar da waɗannan shirye-shirye na gyara don canza matasa zuwa manyan gobe.

TRT Afrika