Bayan daure marasa lafiyar da ake yi da kaca ana tilasta musu yin azumi na kwana 21 zuwa 40 a matsayin hanyar samun waraka, Hoto/ GNA

Kamfanin dillancin labarai na Ghana GNA ya fitar da wani rahoto da ya bayyana yadda wani coci ke azabtar da mutane masu fama da larurar tabin hankali da sunan warkar da su.

Cocin mai suna Pentecostal-Zion da ke Sokode-Akrofu a lardin Volta Region na Ghana ya yi kaurin suna wajen tara mutane maza da mata wadanda iyalansu ba su da karfin iya kai su asibiti domin "ba su kulawar da ta kamata."

Rahoton GNA ya bayyana cewa ana azabtar da masu fama da wannan matsalar ta hanyar daure su da sarkoki da kaca da kwado a jikin rumfar da ake zama don yin ibada a cocin.

''Ana daure kafarsu da hannayensu da manyan kacoci na karfe, don kar su samu damar yin walwala ko guduwa daga wajen,'' a cewar GNA.

Da dama daga cikinsu kan yi fitsari da ba-haya a wajen, duk cikin yanayi na sanyi da zafi da ruwan sama.

Wasu daga cikin majinyatan sun kusan shekara guda a daure a wurin, kuma wani lokacin akan tilasta musu yin azumi na kwana 21 zuwa 40 a matsayin tsarin jiyya don samun waraka.

A hirar da suka yi da Manzo Michael Atiamu, mai aikin warkar da marasa lafiya da ake kawo su cocin, ya ce ana kokarin ganin an samar wa mutanen wurin zama mai kyau kuma ya yi kira da a tallafa musu.

"Ana amfani da kaca ne don tsare su kada su gudu," a cewar Manzo Michael.

Ya kara da cewa akan sa su yi azumin a-kai-a-kai ne don rage musu kuzari saboda a hana su tayar da hankali a wurin, yana mai cewa "ana ba su shayi na lemon tsami da sukari kadan ba tare da burodi ba.

"Sannan a tsawon zamansu a wajen (tsakanin watanni 6 zuwa 12) ba a yarda su sha wani magani ba."

Rashin isasshen abinci da 'yancin motsa jiki da rashin tsafta sun sa wurin ya sanya kunci a zukatan marasa lafiya da ke wajen.

Bayanai sun ce akan bukaci iyalan majinyatan su kai buhun siminti 20 ko kwatankwacin kudin simintin bayan 'yan uwansu sun samu waraka, a wani mataki na tallafa wa aikin gina wurin.

Dokar Kiwon Lafiyar kwakwalwa ta Ghana ta shekarar 2012 ta tanadi cewa mutanen da ke fama da matsalar kwakwalwa "ba za su fuskanci azabtarwa ba ko zalunci ko aikin tilastawa da duk wani nau'in cin zarafi gami da dauri."

A cewar Manzo Atiemu tun shekarar 1970 zuwa yanzu ya warkar da masu fama da matsalar tabin hankali kusan 2,000 daga wurare da dama a fadin Ghana da kuma wasu kasashe da ke makwabtaka irin su Jamhuriyar Dimokuradiyar Togo da Nijeriya da dai sauransu.

Kamfanin dillancin labarai na GNA ya tattauna da wani likitan kwakwalwa a kasar Farfesa Akwasi Osei, wanda ya ce wannan aikin ya saba wa tanadin dokokin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kundin tsarin mulkin Ghana.

Ya ce dole ne a dakatar da shi domin kuwa “majinyatan ba karnukan da za a daure su ba ne.

''Dole a gaggauta sakinsu tare da kai su asibitin kula da kwakwalwa ko da kuwa suna fama da wata matsala da ta shafi rauhanai," in ji Akwasi.

TRT Afrika da abokan hulda