A Cite Soleil, unguwar marasa galihu mafi girma a babban birnin Haiti da ke fama da matsalar ‘yan daba, farkon kwanakin watan Agusta an samu kwararar yara wadanda wasunsu ramammu ne zuwa asibitin Fontaine.
Asibitin na al'umma, wani wuri ne mai kwantar da hankali a wannan bangaren da ya fi talauci a birnin Port-au-Prince sama da shekara 30. Ya zama tamkar mafaka ga mazauna yankin wadanda suke fuskantar barazana kullum daga kungiyoyi masu dauke da makamai da ke iko da wurare da yawa a cikin birnin.
A wannan rana, ma’aikatan jinya suna auna jarirai da kuma yara kanana, suna masu mayar da hankali kan yadda ba sa girma da wuri.
"A ko wace rana, ana kawo tsakanin yara 120 zuwa 160 don yin rigakafi, kuma a wannan gabar muke tantancewa, musamman game da rashin cin abinci mai gina jiki," kamar yadda Jose Ulysseda, mutumin da ya kafa asibitin Fontaine ya shaida wa AFP.
"A wasu lokutan, wadannan yaran tamkar kwarangwal suke kuma da kyar suke numfashi," kamar yadda daraktan ya bayyana, yana mai cewar wannan matsalar ta numfashi tana faruwa ne sakamakon yunwa.
Wadanda matsalarsu ba ta da tsanani sosai, ana ba su magani da tallafin abinci ga iyalansu su koma gida.
Yaran da suke cikin matsanancin hali kuma ana ba su gado a asibiti – wasunsu ana saka musu ruwa ta cikin jijiya –inda suke kwanciya a karkashin kulawar uwayensu, wadanda su ma galibinsu suna fama da yunwa.
Ana ajiye yaran, a wasu lokutan tsawon makonni, har sai nauyinsu ya daidaita.
Yara 40 zuwa 50 suna bukatar agajin abinci a yini, a cewar Ulysse, maimakon kila yara sha biyu a rana daya a shekara hudu ko biyar da suka gabata.
Fuskokin yunwa
Ta hanyar wata kofa, David dan wata 19 da haihuwa, mai sanye da shudiyar riga, yana kallon yadda ake kaiwa da komowa. David na daya daga cikin yaran da ake yi wa magani na tsananin rashin isasshen abinci.
Rikicin ‘yan dabar da ke addabar Haiti ya janyo karuwar matsalar rashin isasshen abinci musamman ga jarirai – har kashi 30 cikin 100 a cikin shekara daya – bisa alkaluman da hukumar UNICEF ta wallafa a watan Mayu.
A cibiyar Fontaine, yaran da alamu suka nuna suna cikin tashin hankali suna tare da duk alamun tsananin yunwa: ramammun fuskoki, hakarkarin da suka taso, kumburarren ciki, kugu mai tsoka da ma kasusuwa mara kwari.
Kusan ko wane yaro daya cikin yara hudu na fama da tamowa a wannan kasa da ta fi talauci a yankin Caribbean, inda sama da yara 115,000 suke fama da yunwar da ke barazana ga rayuwarsu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Rikicin ‘yan daba yana kara sa zuwa aiki ko kasuwa ko kuma kula da yara ya yi wuya a babban birnin Haiti.
Kuma baya ga matsalar tsaron, Haiti tana fama da cutar kwalera.
"Tashin hankali a ko'ina "
"Karin iyaye ba sa iya samar da kula da ta dace da kuma abincin da ya dace ga 'ya'yansu... saboda karuwar tashin hankalin da kungiyoyin masu dauke da makamai ke haddasawa," a cewar Bruno Maes, wakilin Unicef a Haiti, a watan Mayu.
Yayin da maharba ke saman gidaje, kuma ‘yan daba suna yada barazana ta hanyar fyade da garkuwa da mutane da kuma kisa, ya zama abu mai wahala ga iyaye – kuma mai hadari – su kai ‘ya’yansu cibiyoyin bayar da tallafi irin su asibitin Fontaine.
Wasu iyayen "suna barin ‘ya’yansu saboda ba za su iya kula da su ba," in ji Ulysse, yana mai karawa da cewar cibiyar na ci gaba da aiki ne albarkacin taimakon da take samu daga UNICEF.
"Tashin hankali na ko'ina," in ji shi. "Kowa na tsoron kowa."