Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za a wallafa sunayensu idan ba su mika wuya ba./Hoto:Abdullahi Haruna Kiyawa Facebook.

Rundunar 'yan sandan Kano da ke arewacin Nijeriya ta fitar da sunayen wasu mutane da take zargi su ne suke jagorantar harkokin daba a fadin jihar.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa sunayen mutanen a shafinsa na sada zumunta ranar Alhamis da daddare.

Ya umarci mutanen su yi gaggawar mika kansu ga rundunar idan ba haka ba za ta soma nemansu ruwa-a-jallo.

Matsalar daba dai babban batu ne da ya addabi jihar ta Kano, inda bayanai suka nuna cewa 'yan dabar sun kashe gomman mutane a wannan shekarar.

Ana alakanta matsalar kwacen waya a jihar da 'yan daba wadanda ake zargi suna samun goyon bayan wani sashe na 'yan siyasa.

Sai dai sabon gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin murkushe masu aikata laifuka ciki har da 'yan daba.

Ruwa-a-jallo

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce "rundunar 'yan sandan Jihar Kano tana gayyatar wadannan mutane da ake zargi da jagorantar harkar "Daba" da su kai kansu ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kuma a buga nemansu ruwa-a-jallo sannan a kamo su su fuskanci hukunci".

Burakita, Unguwar Dorayi Karama

Messi, da ke Kan Tudun Dala

Dan Boss, Dala Makabarta

Ado Runtu, Tudun Fulani, Bachirawa

Baffa Killer, Mazaunar Tankovi.

Kamilu Duna, Unguwar Adakawav

Chile Mai Doki, Unguwar Tudun Fulani, Bachirawa

Uzaifa, Unguwar Yolai

Hantar Daba, Kwanar Disu

Bahago, Makabarta Kuka Bulukiya

Nasiru Naso, Kofar Wambai

Nazifi Nanaso, Unguwar Zango

Sharu Gambo, Unguwar Sharifai

Sharu Ali, Unguwar Sharifai

Ma’aruf Goma, Unguwar Hanga

Zubairu Mai Dala, Unguwar Yalwa Dala

TRT Afrika