Rawa dodanni dadaddiyar al'ada ce a Afirka. Hoto/Reuters

Daga Charles Mgbolu

Cikin dakikoki kadan wasu bidiyoyi na rawar dodanni masu kwalliya na Afirka ke dauke hankalin jama’a, inda dodannin ke rawa a gaban mutane cikin nishadi.

A cikin irin wadannan bidiyoyin da aka wallafa a shafin wani mai amfani da Tiktok dan kasar Liberia, @Kru_Krou, an ga yadda makadan gangunan da aka yi su da fatun tumaki da kuma masu buga kuge inda aka ga wani dodo yana wata irin rawa yana lankwasa kafafunsa tare da wasu fukafukai a kugunsa.

A al’adar Afirka, ana daukar dodanni a matsayin wasu wakilai na abubuwan bauta na gargajiya saboda ana ganin suna kawo arziki mai amfani. “Ganin dodanni wani lamari ne mai kyau da tsarki,” in ji Christopher Okereke, wanda wani dan gargajiya ne daga kudu maso gabashin Nijeriya.

Ana daukar dodanni a matsayin wasu wakilai na ababen bauta. Hoto/Reuters

”Suna sauya bil adaman da ke saka kayan dodannin zuwa wani abin gaibi. Su ne kashin bayan al’adun Afirka kuma suka bambanta mu da sauran jama’ar duniya,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Sai dai abubuwan da ke tashe daga kasashen yamma na shafe wadannan abubuwa, kuma wadannan abubuwa wadanda a gargajiyance ake wa kallon wakilan ababen bauta a halin yanzu ana mayar da su kayan nishadi a kafafen sada zumunta irin su TikTok.

Kallo a shafukan sada zumunta

Dodanni masu rawa a TikTok a halin yanzu na da miliyoyin masu kallo kuma ana rarraba bidiyoyin har a wajen TikTok.

“Za ka ga dodo a bainar jama’a yana shan barasa ko kuma yana tare da mata suna rawa. Ni da kaina ina shaida wa duk wanda ya damu cewa wadannan ba dodannin gaskiya bane, sakamakon babu wani dodon gaskiya daga Afirka da zai yi irin haka,” in ji Okereke.

Dodanni na kara yin fice a shafin TikTok, lamarin da wasu 'yan gargajiya suke caccaka. Hoto/Reuters

Da alamu damuwarsa ta zama gaskiya, inda wasu bidiyoyin ke nuna wasu abubuwa na mamaki inda dodannin ke durkusa wa ‘yan siyasa suna rokonsu kudi inda wasu ke shan barasa su bugu suna marisa kan hanya.

Wasu daga cikin bidiyoyin ana yin su ne domin a samu masu kallonsu a kafafen watsa labarai inda kuma tuni suka jawo muhawara a tsakanin masu son al’adu.

Damuwarsu ita ce ko wannan al’adar ta Afirka mai karfi na neman gushewa sakamakon irin abubuwa na zamani da ke tashe a kafafen sada zumunta.

“Babbar damuwata ita ce akwai yiwuwar yara masu tasowa za su tashi da tunanin cewa ainahi haka dodannin Afirka suke, sai dai wannan wani abu ne da aka karkatar. Dodanni ba su yin wasanni domin su samu masu kallo a kafafen sada zumunta,” kamar yadda ya kara da cewa.

Sai dai wani mai samar da bidiyoyi a shafukan Facebook Patrick Adigwe ya kalubalanci wannan batun nasa.

Dodanni na taka muhimmiyar rawa a lokacin bukukuwan al'adu na Afirka. Hoto/Reuters

“Al’ada tana tafiya ne da zamanin da muke ciki, kuma wannan tabbaci ne mai kyau kan cewa al’adarmu ta Afirka ba za ta taba gushewa ba sakamakon tana hadewa da karfin shafukan sada zumunta,” kamar yadda Adigwe ya shaida wa TRT Afrika.

“Wannan wata dama ce ta haduwa da yara masu tasowa inda suke, wanda nan ne kafar sada zumunta. Ya kamata mu ji dadi kan cewa wannan na jawo suna kara neman sani.

Yara masu tasowa suna yin tambayoyi tare da kokarin sanin asalinsu, wanda akwai yiwuwar ba su taba saninsa ba ma idan ba ta kafar sada zumunta ba.

“Dodanni na taka rawa daban-daban,” in ji Okereke. “Eh, za su iya nishadantarwa, sai dai akwai bukatar a yi taka-tsan-tsan kan cewa kada a kuskura a yi amfani da dodon da ake amfani wurin ruhanai domin rawa a TikTok; wannan shi ne abin da matasan TikTok suke yi wanda ba daidai bane, kuma wannan ne abin da ya kamata a yi gaggawar gyarawa domin kare al’ada,” in ji shi.

Muhawara kan rawar da dodanni ke yi a TikTok na da wuyar samun daidaito.

Domin samun ci gaban al’ada, akwai bukatar yara masu tasowa su zage damtse su ci gaba da tafiyar da al’adun Afirka, sai dai za su iya yin haka ne kawai idan aka bi musu ta hanyar da su ka fi ganewa.

Sai dai dole ne su rinka yin taka-tsan-tsan, saboda zai zama cewa abin banza ne kokarin kare wata al’ada da ba ta dauke da wani karsashi na gargajiya.

TRT Afrika