A yayin da yawan al’ummar Nijeriya ke karuwa da sauri kamar yadda alkaluma ke nunawa, wasu masana na nuna damuwa kan hakan, inda suke cewa yawan al’ummar kasar ka iya zame mata barazana idan ba a dauki matakai ba.
Nijeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka, kuma ita ce kasar bakaken fata mafi yawan jama’a a duniya.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya na ranar Litinin 10 ga watan Yulin 2023 sun ce yawan alummar Nijeriya ya kai miliyan 221,546,156, kamar yadda shafin Worldometer ya rawaito.
Sai dai, dama Nijeriya na shirin gudanar da kidayar jama’a a kasar, irin ta ta farko tun bayan wacce aka yi a shekarar 2006.
Wadannan sabbin alkaluma na yawan jama’a na Nijeriya sun fito ne a daidai lokacin da ake bikin Ranar Yawan Al’umma ta Duniya ta 2023, wacce ake yi ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara.
Makasudin bikin ranar shi ne tunatar da duniya yadda za a warware matsalolin da yawan al’umma ke jawowa, inda ake so a mayar da hankali kan daidaiton jinsi da tallafawa mata da ‘yan mata don samun rayuwa mai inganci.
Masana tattalin arziki sun rabu gida biyu a kan batun yawan al’umma: masu ganin yawan jama’a matsala ce ga tattalin arzikin kasa.
Sai kuma masu ganin cewa babu arzikin da ya wuce yawan jama’a a duniya, kamar yadda masanin tattalin arziki a Nijeriya Dokta Isa Abdulla ya shaida wa TRT Hausa.
Amma a yayin da ake ganin kamar yawan al’ummar Nijeriya ka iya zame mata matsala, masana na ganin akwai hanyoyin da kasar za ta bi don cin gajiyar hakan.
Bunkasa mutane a fannin kimiyya da fasaha
Masana sun ce dole ne gwamnatoci su bai wa jama'a ilimi mai nagarta a fannin kimiyya da fasaha idan suna son cin moriyar yawan al’ummarsu.
“Shahararren masani kan tattalin arziki Alfred Marshal na cewa idan dan adam yana da rai da lafiya da ilimi da kuma fikira, to ko a jikin itace ko a jikin kasa ne zai san yadda zai samu abinci.
Kenan abin da ya zama dole ga gwamnatocin nan shi ne a tabbatar ba a bar matasa suna gararamba a gari ba, kar a bar su su sha kwaya, ko su zama ‘yan barandan siyasa.
A ba su ilimi na zamani da duniya ke bukata. A koya musu sana’o’i na dogaro da kansu irin wanda ake amfani da su a duniya a yau.
Alal misali, masanin ya ce idan aka dauki kasar Jamus, za a ga cewa ba ta da ma’adanai kamar su man fetur da sauran su, amma kusan ita ce ta farko a karfin tattalin arziki a Tarayyar Turai saboda bunkasa ilimin kimiyya da fasaha," in ji Dokta Isa Abdulla.
Kada a bar matasa kara-zube
Masanin ya ce bai kamata a bar matasa masu hazaka suna zauna kara-zube yana mai cewa "a nemo su a gyara musu fikirarsu a koya musu sana’a mai karfi."
Dokta Isa ya kara da cewa “Ana iya amfani da matasan Nijeriya a kafa masana’antu a horar da su su dinga samar mana da mafi yawan abubuwan da kasar ke shigar da su daga kasashen waje.
“Za a iya bai wa matasa horo wajen samar mana da kayayyakin sawa na zamani da wayoyi da sauran abubuwa.”
Tanadar isassun abubuwan bukatar rayuwa
Shi ma wani masanin tattalin arzikin Dokta Auwal Mahmud ya ce kasa irin Nijeriya da al’ummarta ke karuwa da sauri-sauri, dole ne ta dinga tanadin abubuwan bukatar rayuwa.
Sai dai abin tambayar shi ne ko Nijeriya tana irin wannan tanadi, kamar na isassun makarantu da kayayyakin more rayuwa, da wutar lantarki da asibitoci da likitocin da duk za a bukata?
Ya ce a misali, wutar lantarkin Nijeriya “tun shekarar 1960 lokacin muna da mutum miliyan 45 ake samar da megawat 4,000, amma a yanzu da yawanmu ya kai miliyan 216 amma kuma yawan wutar lantarki bai karu fiye da megawatt 4,000 ba.”
Ya jaddada cewa don haka dole sai gwamnati ta samar da dukkan abubuwan more rayuwa isassu da ake bukata kafin a ji dadin yawan jama’ar kasar.
Isasshen shiri
Ana bukatar isasshen shiri na a kalla shekara goma na hasashen yawan karuwar al’umma ta yadda idan aka samu karuwar za a amfana da su.
“Idan ba a samu wannan ba, to duk abin da zai samu zai zamanto nauyi ne zalla don haka sai ya zame mana bala’i maimakon dadi,” a cewar Dokta Mahmud.
Wasu muhimman bayanai kan yawan al'ummar Nijeriya
- Yawan mutanen Nijeriya ya zuwa watan Yulin 2023 ya kai 221,546,156
- Yawan al’ummar Nijeriya shi ne kashi 2.64 cikin 100 na al’ummar duniya
- Nijeriya ita ce kasa ta shida mafi yawan jama’a a duniya
- Girman fadin Nijeriya ya kai 910,770 sikwaya kilomita
- Kashi 52 cikin 100 na mutanen kasar na zaune ne a birane
- Birane 10 da suka fi yawan jama’a a kasar su ne Legas, Kano, Ibadan, Kaduna, Fatakwal Benin, Maiduguri, Zariya, Aba da kuma Jos.