Wasu daga cikin fitattu kuma masana daga arewacin Nijeriya sun aika wasiƙa ga Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da Majalisar Tarayyar Nijeriya inda suke gargaɗi kan batun ƙulla yarjejeniya da Amurka da Faransa da ake zargin za su yi da Nijeriya domin mayar da sansanoninsu.
A kwanakin baya ne wasu rahotanni suka rinƙa yawo waɗanda ke nuna cewa Shugaban Nijeriya Tinubu na shirin amincewa da ƙasashen su mayar da manyan sansanoninsu Nijeriya bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi hannun riga da ƙasashen.
A wata takarda wadda aka rubuta 3 ga watan Mayun 2024, masanan na arewa sun buƙaci gwamnatin ta guji ɗaukar wannan matakin.
Daga cikin waɗanda suka sa wa wasiƙar hannu akwai tsohon shugaban Hukumar Zaɓen Nijeriya Attahiru Jega da shugaban ƙungiyar CISLAC a Nijeriya da ke yaƙi da cin hanci da rashawa Auwal Musa Rafsanjani da kuma tsohon ministan man fetur a Nijeriya Kabiru Chafe.
A cikin wasiƙar, sun nuna damuwarsu kan cewa akwai yiwuwar gwamnatin Nijeriyar ta amince da wannan kudirin wanda suka ce zai iya kawo matsala a tsarin tsaron ƙasar.
Sun jaddada cewa ayyukan da sojojin Amurka suke yi a yankin na Sahel ya gaza samar da zaman lafiya, hasali ma sai ya ƙara taɓarɓarar da al’amura.
Wasiƙar ta yi zargin cewa ƙasashen Amurka da Faransa suna ta kamun ƙafa a wurin Nijeriya da wasu ƙasashe a yankin domin ba su wurin da za su kai dakarunsu da aka kora daga Nijar.
Dattawan sun nuna damuwarsu dangane da matsalolin tattalin arziki da na muhalli da za su iya tasowa idan har Nijeriya ta amince ta karɓi sojojin na Faransa da Amurka.
“Ta fannin tattalin arziƙi, zaman waɗannan sansanonin za su iya karkatar da kuɗaɗen gwamnati daga ayyuka a wurare masu muhimmanci da suka shafi ilimi da lafiya da ababen more rayuwa a koma kula da waɗannan sojojin.
“Wannan karkatarwar ta albarkatu za ta iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da kuma ta'azzara talauci a kasar da yawancin al'ummar kasar ke rayuwa a cikin mawuyacin hali,” in ji masanan.
“Bugu da kari, karbar bakuncin sojojin ƙasashen waje yakan haifar da hauhawar farashi da tsadar rayuwa a yankunan cikin gida, wanda hakan ke shafar masu ƙaramin karfi.
“Ta ɓangaren muhalli, ginawa da aiki da sansanonin soji na iya haifar da mummunar lalacewar muhalli. Wannan ya hada da sare dazuzzuka da zaizayar kasa da gurɓacewar ruwa da asarar halittu masu rai, wadanda duka waɗannan suna cutar da al’ummomin da ke noma da ‘yan asalin kasar,” in ji su.