Dakarun da ke gadin Teku a Turkiyya sun kubutar da bakin-haure akalla 58 daga Tekun Aegean bayan hukumomin Girka sun kore su zuwa yankin ruwa na Turkiyya.
Masu kula da tekun sun ceto bakin-haure 45 daga cikin wani kwale-kwalen roba ranar Asabar, a gabar teku da ke lardin Seferihisar na yammacin Izmir.
Kazalika an ceto mutum goma sha uku a gabar teku ta yankin Dikili a wani aikin kubutar da bakin-haure na daban da masu gadin tekun suka gudanar.
Haramtaccen aikin Girka
Turkiyya da Tarayyar Turai da kuma masu sanya ido na kasashen duniya sun sha sukar Girka saboda korar bakin-haure ta haramtacciyar hanya.
Sun ce hakan ya saba wa dokokin kasashen duniya inda kasar ta Girka ke jefa rayukan mutanen, ciki har da mata da kananan yara, cikin hatsari.
Turkiyya ta kasance wata muhimmiyar hanya da masu neman zuwa Turai ta haramtacciyar hanya suke hutawa kafin su tsallaka Turai, musamman wadanda suke tsere wa yake-yake da cin zarafin da ake yi a kasashensu.