Majalisar Dinkin Duniya na fatan kasashen Afirka za su samar da isassun matakan dakile wariyar launin fata. / Hoto: AP

Wani rahoto da ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya bayyana cewa har yanzu 'yan Afirka bakaken fata suna fuskantar "gagarumin kalubale" wajen a dama da su a harkokin da suka shafi al’umma a kasashe katare saboda "tsarin wariyar launin fata da nuna kyama da ya samo asali daga mulkin mallaka da suka gada."

Rahoton ya bayyana cewa, "tsarin na wariyar launin fata na ci gaba da yin tasiri ga mutanen da suka fito daga kasashen Afirka ta kowacce fuska a rayuwa," a cewar sanarwar OHCHR a ranar Talata.

Yawan mace-macen 'yan Afirka da ake samu a yayin ko bayan mu'amalarsu da jami'an tsaro a kasashen katare na ci gaba da karuwa, ko da yake alamu sun yi nuni da cewa an dan samu ci gaba wajen hukunta wadanda ke aikata laifin - ba tare da la’akari da tsawaita duk wasu jayayya daga iyalai ke neman daukar fansa da wani sakamako ba.

"Idan ana so a shawo kan wannan batu na nuna wariyar launin fata, dole ne sai kasashen ketare sun hanzarta daukar matakai masu ma'ana tare da bai wa al'ummar Afirka dama don su ba da gudumawarsu a kowane fanni na harkokin jama’a a kasashen," a cewar babban kwamishinan kare hakkin bil'adama na MDD Volker Turk.

"Muhimmin abin da kasashen nan za su mayar da hankali akai shi ne, tabbatar da cewa bukatu da gogewa da kuma kwarewar 'yan Afirka sun ta’allaka ne kan tsara manufofi da aiwatarwa da kuma kimantawa," ya ce. "Babu wani abu da za a iya sani game da su in ba tare da su ba," in ji shi.

Cikas

Rahoton ya ba da kwararan misalai kan shirye-shirye wadanda aka aiwatar da su don karfafa shigar 'yan Afirka cikin harkokin jama'a a wasu kasashe, in ji sanarwar.

Kazalika, rahoton ya kuma yi nuni kan ire-iren cikas da ake samu da kuma rashin samar da yanayi da tsaron da za su bai wa 'yan Afirka damar nuna kwazon da kwarewarsu da za su yi tasiri wajen daukar matakai da shawarwari."

‘’Nuna kabilanci da wariyar launin fata da sa ido da cin zarafi da tsoratarwa da kamawa da kuma cin zarafin 'yan Afirka da kungiyoyin fafutuka ta farar hula a Afirka na fuskantar kalubale na kin ba su dama a matsayi da matakai daban-daban da suka shafi al’umma a kasashen ketare da dama," a cewarTurk.

Ya bukaci kasashen da su fitar da kwararan matakan doka da tsare-tsare da kuma kafa hukumomi da za su dakile tsarin nuna wariyar launin fata a kowane fanni na rayuwa, gami da doka wacce za a tabbatar kan batun.

Ana sa ran gabatar da rahoton ga hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar 5 ga watan Oktoba.

TRT Afrika