Tsananin tasirin sauyin yanayi a 2023: Kira ga duniya ta dauki matakin gaggawa kan lamarin

Tsananin tasirin sauyin yanayi a 2023: Kira ga duniya ta dauki matakin gaggawa kan lamarin

Sauyin yanayi ya kasance wani lamari na gaggawa wanda ake bukatar kasashen duniya su tashi tsaye a kansa domin daukar matakai.
Dubban mutane suka rasu sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a Libiya. Hoto/Reuters

Daga Peter Asare-Nuamah

Tun daga 18 zuwa 26 ga watan Satumbar 2023, shugabannin duniya sun gudanar da taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya UNGA a birnin New York.

Wannan taron yana bayar da dama a yi kira ga shugabannin duniya su farka dangane da irin barnar da sauyin yanayi yake yi tare da daukar matakan da suka dace don dakile sauyin yanayin da bala’o’in da muhalli ke fuskanta, haka kuma da tasirin hakan kan tattalin arzikin duniya baki daya da kuma kasashe masu tasowa.

Dole ne Shugabannin kasashen da lamarin ya fi tasiri a Afirka da sauran sassan duniya a taron UNGA su fi bayar da fifiko kan tattaunawar da za ta bayar da mafita ga kasashe masu tasowa.

Tattalin arzikin duniya na farfadowa a hankali daga irin tasirin da annobar korona ta yi, duk da haka kasashe masu tasowa suna ta fama da tasirin da annobar ta yi musu na tsawon lokaci.

Tare da wannan, kasashe masu tasowa sun fuskanci matsalolin sauyin yanayi matuka, wanda hakan ya kara ta’azara damar da suke da ita ta dakile kalubalen da ke kawo cikas ga tattalin arziki da kuma jama’a.

Ba shakka, shekarar 2023 ta fuskanci matsaloli masu tsanani na sauyin yanayi.

Tsananin zafin bazara da aka yi a Turai da Amurka da fari da wutar dajin da aka yi a Sifaniya da wasu sassan Canada da Arewacin Afirka duk suna daga cikin matsalolin sauyin yanayi a 2023.

Duk da haka, kasashe masu tasowa na fuskantar barazana mafi girma da kuma matsalolin sauyin yanayi masu tsauri. Misali na bayyane shi ne ambaliyar ruwan da aka yi a gabashin Libiya wadda ta kashe dubban mutane.

Haka kuma a farkon watan Janairu, kasashen Uganda da Rwanda da Kongo sun fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni.

Guguwar Freddy wadda ta yi matukar barna a Malawi ta jawo asarar rayuka sama da 1,400. Hoto/Reuters

Akwai mahaukaciyar guguwa da ta fada wa gefen teku a Zimbabwe da Mozambique da Malawi da Madagascar a watan Fabrairu.

A watan Maris, kasashen Peru da Ecuador da ke Kudancin Amurka sun fuskanci mahaukaciyar guguwar Yaku inda Indiya da Bangladesh da Myanmar kuma suka fuskanci guguwar Mocha a watan Mayu. Ba shakka, a daidai lokacin da tasirin sauyin yanayi ke karuwa, haka kuma bala’o’in ke karuwa.

A wani abu na tarihi, Amurka ta fuskanci bala’o’i 23 daga Janairu zuwa Satumbar 2023, wanda hakan ya wuce abin da aka samu a 2020 na bala’o’i 22, inda aka tafka asarar dala biliyan 57.6 a tattalin arziki.

Misali guguwar Freddy ta yi sanadin asarar dala biliyan 1.5 a kasashen da ke kudancin Afirka inda guguwar Mocha ta jawo asarar dala biliyan 1.1 a kasashen Asia. Bugu da kari kan asarar da aka yi ta tattalin arziki, adadin wadanda suka mutu sakamakon sauyin yanayin ya karu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ya wuce 11,300.

Tsananin matsalar sauyin yanayin ta jawo rashin abinci da talauci, lamarin da ya haddasa hijira musamman a wuraren da rikici ya daidaita kamar Sudan da Libiya.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a taron UNGA ya bukaci kasashen duniya su dauki mataki kan sauyin yanayi. Hoto/Reuters

Haka kuma sauyin yanayi yana tasiri matuka kan muradan karni, inda lamarin ke lalata ci gaban da aka samu musamman a kasashe masu tasowa. Akwai bukatar shugabannin duniya su tashi tsaye fiye da kowane lokaci domin kawo sauyi ga sauyin yanayi.

Akwai bukatar UNGA ta lura da yadda ake samun karuwar matsalolin sauyin yanayi da kuma matakan da za a iya dauka domin dakile su a kasashe masu tasowa.

Akwai kuma bukatar a bayar da kudi ga cibiyoyi da tsare-tsare wadanda suka hada da Green Climate Fund domin mayar da hankali kan bincike mai tasiri wanda zai iya kawo sauyi ga al’ummomin da ke cikin hatsari.

Haka kuma, akwai bukatar shugabannin duniya su mayar da hankali kan ci gaban al’umma.

Muhimmin abu, dole ne kasashen da suka ci gaba su dauki alhakin gyaran wuraren da muhalli ya lalata sakamakon ayyukan da suka yi.

Wannan ya hada da alkawarin da suka yi na dala miliyan 100 a duk shekara ga sauyin yanayi a kasashen da ke tasowa.

Akwai bukatar samar da kayayyakin sa ido kan sauyin yanayi ta bangaren kimiyya da wayar da kai domin kai su yankuna masu tasowa wadanda ke fama da matsaloli na sauyin yanayi.

Dakta Peter Asare-Nuamah, malami ne a Jami’ar Ci Gaba Mai Dorewa da ke Ghana kuma babban mai bincike ne a Cibiyar Bincike kan Ci gaba ta Jami’ar Bonn da ke Jamus.

Togajiya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayoyi da mahangar iditocin TRT Afrika ba.

TRT Afrika