Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS.
An sanar da hakan ne a yayin taron kungiyar na 63 wanda ake yi a Guinea Bissau a yau Lahadi.
Tinubu ya karbi jagorancin kungiyar ne daga hannun Shugaban na Guinea Bissau Umaro Embalo.
Wannan ne karo na farko da shugaban ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Yaki da juyin mulki
Da yake jawabi bayan ya zama shugaban kungiyar ECOWAS, Shugaba Tinubu ya ce dole kasashen yankin su yaki dabi'ar juyin mulkin soji.
Kazalika ya yi kira da a samar da tsarin tattalin arzikin yankin wanda 'yan kasuwa masu zaman kansu za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa shi.
"A matsayina na shugaban wannan muhimmyar gamayya, ina jaddada sadaukarwata da kuma ta kasata wajen tabbatar da zaman lafiya da ci-gaba a yayin da muke neman hadin-kai don magance matsalolin kasashenmu irin su rashin tsaro, bunkasa tattalin arziki da ci-gaba mai dorewa," in ji Shugaba Tinubu.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Lagos, inda ya ce sun ci abinci tare kuma "mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu."
A wancan lokacin, shugaban Nijeriya ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da kasar jagora ga sauran kasashen nahiyar Afirka.