Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar 36 a ranar Alhamis a Fadar Aso Rock.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shawarci gwamnonin ƙasar da su yi koyi da abin da Jihar Kano ta yi na magance matsalar masu ɓoye abinci “don samun ƙazamar riba”.

Tinubu, wanda ya fadi hakan a taron da ya yi da gwamnonin ƙasar 36 a ranar Alhamis a Fadar Aso Rock, sun kuma yi alkawarin yin aiki tare shi da gwamnonin don warware matsalolin da ƙasar ke fama da su da kuma magance halin matsin tattalin arziki da al’umma ke ciki.

Duka mahalarta da suka haɗa har da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, sun amince da batun magance wasu manyan matsalolin da ake fama da su a ƙasar musamman hauhawar farashin kayan abinci da kuma rashin tsaro.

Ga muhimman abubuwan da Shugaba Tinubu ya ce wa gwamnonin su yi:

Magance rashin tsaro

Da yake magana a kan yadda za a magance matsalar rashin tsaro wacce ya ce tana shafar harkokin noma da samar da abinci, Shugaba Tinubu ya yi alkawura da suka haɗa da:

  • Za a ƙara ɗaukar jami’an ƴan sanda don ƙarfafa rundunar
  • Shugaba Tinubu zai yi aiki da gwamnoni da Majalisar Wakilai ta ƙasa wajen samar da wata hanya da za ta samar da ‘yan sandan Jihohi maimakon ‘yan banga da ake amfani da su a wasu jihohin
  • Shugaban ya bukaci Gwamnonin da su ƙarfafa jami’an da ke kula da gandun daji tare da ba su makamai domin kare dukkan dazuka daga masu aikata laifuka
  • Samar da tsare-tsaren da ‘yan sandan jihohi za su bi da kuma magance matsalolin tsaro da za a ci gaba da tattaunawa a Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa.

Hauhawar farashin kayan abinci

Shugaban Kasar ya umarci Gwamnatocin Jihohi da na tarayya da su haɗa kai wajen samar da ƙarin abincin da ake nomawa a cikin ƙasar, inda ya yi watsi da batun shigar da abinci.

Sannan ya ce ya kamata a dinga ƙayyade farashi ta yadda masu samar da abinci a ƙasar za su samu ƙwarin gwiwar samar da mai yawa.

Kazalika Shugaba Tinubu ya shawarci gwamnonin da su kwaikwayi abin da Jihar Kano ta yi na magance ɓoye abinci don samun ƙazamar riba da ƴan kasuwa ke yi, tare da umartar Sufeto-Janar na Ƴan sanda da Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro da Hukumar DSS, saka ido a kan wuraren da ake ɓoye abinci a faɗin ƙasar tare da dakatar da masu yin hakan.

Kula da bunƙasar dabbobi

Shugaba Tinubu ya kuma nemi gwamnonin da su mayar da hankali wajen ganin bunƙasar dabbobi a jihohinsu da ƙara samar da su musamman dangin kaji da kifaye.

Biyan kudaden ma’aikata

Shugaban ya roki Gwamnonin da su tabbatar da cewa an biya duk wani bashin albashin ma’aikata da kuma kuɗaɗen tallafi ga ma’aikata da ‘yan fansho a matsayin hanyar sanya kuɗi a hannun jama’a tun da yanzu jihohi suna samun ƙarin kuɗaɗen shiga na FAAC duk wata.

“Ku kashe kudin, kada ku kashe mutane,” ya gaya wa gwamnonin.

Shugaba Tinubu ya roki gwamnoni da su ƙara samar wa matasa damarmakin tattalin arziki a jihohinsu domin su ƙara himma.

TRT Afrika