Ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan Rediyon Freedom na jihar Kaduna, wadda aka watsa ranar Talata. Hoto: El-Rufai X

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce zai iya rantsuwa da Al’kur’ani Mai Tsarki don ya wanke kansa, kan zargin cewa ya yi almundahana da kuɗaɗen gwamnati a lokacin mulkinsa.

Ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan Rediyon Freedom na jihar Kaduna, wadda aka watsa ranar Talata.

El-Rufai ya ce yana sane da duk “wani sharri da bi-ta-da-ƙulli da iskanci da ke fitowa daga Kaduna, amma na yi shiru ina kallon ikon Allah domin ni duk abin da na shiga yi a rayuwata kullum ina roƙon Allah Ya shige min gaba, Ya taimake ni, amma ina kokarin na ga ban yi ba daidai ba ko kuma cin amanar da al’umma suka ba ni.”

El-Rufai ya ce ya sha fadar cewa duk ranar da shugabannin jihar Kaduna suka shirya su je su yi alwala su dauki Al’kur’ani su rantse cewa ba su saci kudin jihar Kaduna ba, “ni zan iya rantsewa don na san ban shiga aikin gwamnati don na daukar wa al’umma kudi ba,” in ji shi.

Kalaman nasa sun biyo bayan rahoton da a kwanakin baya majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar da ke zargin gwamnatinsa da almubazzaranci da naira biliyan 423 a tsawon shekaru takwas da ta yi tana mulki.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar ministocinsa a wasu lokuta sun musanta zargin, inda suka bayyana rahoton na majalisar a matsayin na siyasa.

El-Rufai ya shaida wa Freedom Radion cewa shi bai dauki siyasa a matsayin sana’a ba, ya dauke ta a matsayin hanya ta yi wa al’umma aiki, “don haka duk wanda ke neman kudin cefane ko ya samu kudi don tura ‘ya’yansa makaranta ko ya kai iyalansa umra da hajji to bai kamata ya shiga siyasa ba.

“Wanda ya san yana da hakuri da abin da Allah Ya ba shi to shi ya kamata ya shiga siyasa don shugabanci na siayasa amana ce da Allah Ya dora wa mutane.

“Ni dama tun kafin na shiga siaysa ina da abubuwan da nake yi a fannina na Quantity Survey da kimiyya da fasaha, kuma tun ina gwamnati muke jawo hankalin matasa su shiga fannin kimiyya da fasaha don dogaro da kai.

Da aka tambayi tsohon gwamnan kan batun yadda rayuwarsa ta sauya bayan sauka daga mulki, sai ya ce a yanzu ya fi samun lokacin kansa da na kula da iyalansa saboda raguwar aiki.

TRT Afrika