Hukumomi a Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya sun ce an ceto kimanin fasinjoji sittin daga kusan mutum 300 da kwale-kwale ya yi hatsari da su a ƙaramar hukumar Mokwa ranar Talata da maraice.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Mokwa, Abubakar Dakani, ya fitar ranar Laraba ta ce kwale-kwalen ya kife ne a kogin Gbajibo ranar Talata da maraice.
Dakani ya ƙara da cewa mutanen da ke cikin kwale-kwalen suna kan hanyarsu daga ƙauyen Mundi zuwa Gbajibo domin gudanar da bikin Mauludu lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce shugaban ƙaramar hukumar ta Mokwa Abdullahi Muregi ya tabbatar da gano gawawwaki 60, tare da mutum 10 da suka tsallake rjiya da baya.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Neja Abdullahi Baba, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran na Anadolu cewa kawo yanzu ana neman fiye da mutum 150 da suka ɓata bayan kifewar kwale-kwalen.
Irin wannan lamari ya faru ƙaramar hukumar ta Mokwa a watan Satumban da ya gabata inda mutum aƙalla 26 suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale.