Ministan Harkokin Waje da Haɗin-Kai na Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana yadda Faransa take gudanar da "sabon salon mulkin-mallaka", inda ya zarge ta da goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.
Babban jami'in diflomasiyyar na Faransa ya yi jawabi a wajen Babban Taron MDD Karo na 79 a Amurka a ranar Litinin.
Ya tunatar da cewa "yankin Sahel ya faɗa rikici sama da shekaru 10 da ke barazana ga wanzuwar ƙasashen yankin", inda ya roƙi manyan ƙasashen duniya da su kawo ɗauki ga ƙoƙarin kawar da ta'addanci a yankin Sahel.
"Nijar na sake suka da babbar murya ga waɗannan ayyuka (na ta'addanci) da nuna adawa da duk wani nau'i na goyon bayan ta'addanci," in ji Bakary Yaou Sangare.
Sukurkucewar kawance
Wannan ne wajen ƙalubalantar sabon salon mulkin-mallaka da Faransa ke amfani da shi, wanda ke bayar da bayanai, horo, kuɗaɗe da makamai ga ƙungiyoyin ta'adda a yankin Sahel," in ji shi.
Ministan harkokin wajen ya soki "Yadda Ukraine ta goyi bayan harin ta'addanci da ƙawancen 'yan ta'adda suka kai a yankin Tinzaouaten da ke Mali."
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ma ya zargi Faransa a watan Agustan da ya gabata da neman wargaza ƙasarsa da goyon bayan ta'addanci a Yammacin Afirka. Mahukunta a Paris ba su mayar da martani ga wannan zargi ba.
Alaƙar diflomasiyya tsakanin Faransa da ƙasar da ta yi wa mulkin-mallaka ta lalace tun watan Yulin 2023, a lokacin da sojoji suka ƙwace mulki a ƙasar ta Yammacin Afirka.
Faransa na fuskantar irin wannan tarnaƙi da ƙasashen Mali da Burkina Faso bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasashen.