Ta yaya dimbin bashin da Ghana ta karbo daga China yake shafar 'yan kasar?

Ta yaya dimbin bashin da Ghana ta karbo daga China yake shafar 'yan kasar?

Ghana na neman kasar China ta saukaka mata kan bashin da take bin ta.
Photo/ AA

Ministan Kudi na Ghana Ken Ofori-Atta na yin ziyara a China domin tattaunawa kan yadda za a saukaka wa kasarsa bashin da ake bin ta.

Ana sa ran gudanar da tattaunawar ranar Alhamis da Juma’a kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

China na bin Ghana bashin dala biliyan 43.9, a cewar babban bankin kasar, a rahoton da ya fitar a Nuwamban 2022.

Dakta Patrick Okpoku Asuming, wanda malami ne a Jami’ar kasuwanci ta Ghana ya shaida wa TRT Afrika cewa bashin da ake bin kasar ya kai kusan kashi 94 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikinta.

Bashin da ake bin kasar "ya karu matuka kuma muna amfani da kashi 60 cikin 100 na kudin shigar kasar wajen biyan bashi wanda ba abu ne da zai dore ba,” kamar yadda Dakta Asuming ya bayyana.

Malamin Jami’ar ya kara da cewa kasar ta rasa gurbi a babbar kasuwar hannayen jari ta duniya saboda karancin kudi.

Jinkiri wajen ci gaba

Dr Asuming ya bayyana cewa akwai bukatar kasar ta rage kashe kudi kan ababen more rayuwa ko da yake hakan kuma zai kawo tsaiko wurin ci gabanta.

Darajar kudin kasar wato Cedi za ta ragu sosai sakamakon karuwar bashi da kuma rashin dama a kasuwar hannayen jari ta duniya.

Saboda kasar ta dogara ne da shigo da kayayyakin da aka kera da kuma makamashi, haka kuma farashin kayayyaki ya tashi sosai.

Balkisu Mohammed, wata matar aure da ke aiki a matsayin manaja a wani gidan abinci, ta bayyana cewa da kyar take tafiyar da kasuwancinta saboda matsin tattalin arziki.

Duk da cewa ta yi digiri na biyu fannin Ilimin kula da ma’aikata, Balkisu ta bayyana cewa tana samun Cedi 25,00 inda ta shaida wa TRT Afrika cewa kudin ba za su ishe ta ma zuba wa motarta fetur ba inda ta ce tana kashe har cedi 60 kan mai a mako.

“Idan gwamnati za ta yi abu a fili kan abin da za su ba China domin su samu saukin bashi, za mu yarda,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Me ya sa wannan ke da muhimmanci?

Baya ga neman China ta sake fasalin bashin Ghana a wata hanya da Ghana za ta iya biya cikin sauki, ana sa ran ministan kudi na kasar zai je kuma ya tattauna da wasu masu bayar da bashin.

“China ce ta fi kaso mai tsoka na bashin da ake bin Ghana kuma wasu mambobin kungiyar G20 sun ce sai China ta amince da bukatun Ghana kafin su ma su bari a yi tattaunawar da su,” kamar yadda Dakta Asuming ya shaida wa TRT Afrika.

Ya kara da cewa tattaunawar wani mataki ne mai muhimmanci na samun lamuni na dala biliyan uku wanda gwamnati ke son amfani da shi domin daidaita lamura da kuma sake gina tattalin arzikin kasar.

Amma ga ‘yan Ghana kamar Balkisu, yana da muhimmanci ga ministan kudi ya yi abubuwa a zahiri ya bar ‘yan Ghana su san abin da kasar za ta bayar idan za a saukaka mata. “Dama kasuwar Ghana ta cika da kayayyakin China. Za su ci gaba da kawo karin kayayyakin China ne a lokacin da Nana Akufo-Addo ke cewa mu ci abin da muke samarwa,” in ji ta.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince