Sudan ta yi watsi da wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya zargi ɓangarorin da ke gaba da juna da aikata laifuka da dama waɗanda suka take haƙƙin bil’adama da kan iya zama laifukan yaƙi.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar da yamma, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce rahoton “ya wuce gona da iri.”
Rikicin Sudan ya fara ne a lokacin da rikici tsakanin sojoji da RSF ya ƙara ta’azzara zuwa wani babban yaƙi. Fararen hula na fuskantar matsalar yunwa, gudun hijira da kuma cututtuka bayan watanni 17 na yakin.
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na Sudan a ranar Juma’a ya bayyana cewa duka ɓangarorin sun aikata laifuka “waɗanda suka shafi take haƙƙin bil’adama,” waɗanda za su iya zama laifukan yaƙi.
Ofishin ya yi kira kan dakatar da kai hari nan take kan farar hula tare da buƙatar kai dakaru waɗanda ba ruwansu da kowane ɓangare domin kare farar hula.
Haka kuma ofishin ya buƙaci faɗaɗa takunkumin nan na makamai na Darfur wanda ke ƙunshe a yarjejeniyar tsaro ta majalisar domin faɗaɗa shi zuwa Sudan.
Wannan matakin an samar da shi ne domin daƙile yawon da makamai ke yi, da sauran tallafin da ɓangarorin da ke rikici da juna ke yi domin rage ƙaruwar wannan rikicin.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan ɗin ta caccaki ofishin na MDD da ke ƙasar inda ta zarge shi da rashin nuna ƙwarewa wurin gudanar da ayyukansa ta hanyar wallafa rahoton kafin miƙa shi ga Hukumar Kare Haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ma’aikatar ta bayyana rahoton na MDD ɗin a matsayin na “siyasa ba wanda na shari’a ba,” tare da jaddada cewa rahoton ya wuce gona da iri.