Tsawon shekaru Somalia na fama da matsalar tsaro, inda kungiyoyin ta'adda na Al-Shabab da Daesh ISIS ke yin babbar barazana. / Photo: AFP 

Dakarun Somalia sun kashe aƙalla 'yan ta'addar Al-Shabab 304 a farmakan da suka kai wa ƙuniyar mai alaƙa da Al-Qaeda a watanni biyun da suka gabata, kamar yadda jami'ai suka sanar.

Farmakan waɗanda Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Kasa ta kai, da tallafin sojojin ƙasar da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, an kai su ne a lardunan kudanci da tsakiyar kasar.

Hukumar leken asirin ta ce ta kai farmaki tare da haɗin gwiwar sojoji a yankin Yaaqle dake yankin Middle Shabelle inda aka nufi 'yan ta'adda, an kuma kashe a kalla 27 tare da jikkata wasu 30.

"Wannan farmaki, wanda na ɗaya daga ayyukan kakkaɓe 'yan ta'adda a yankin da ake ci gaba da yi, kuma ana nufar mambobin Khawarij da ba su daina kai wa jama'ar Somalia hari ba." in ji wata sanarwa da ta ayyana Al-Shabab a matsayin Khawarijawa.

An kuɓutar da garuruwa

Hukumar ta kuma ce ana sanar da fararen hula da su ƙaurace wa wuraren da 'yan ta'addar ke gudanar da ayyuka a yankin.

Sama da 'yan ta'addar Al-Shabab aka kashe tare da jikkata wasu da dama a irin wannan farmaki da aka kai a Bida Isse da Gerille da ke ƙarƙashin garin Eeldheer da aka kuɓutar a Galmudud a farkon wata Oktoba, kamar yadda shugaban rundunar sojin Somalia ya sanar.

Kazalika an kashe 'yan ta'ada sama da 95 a kauyuka bakwai da aka kubutar a wannan wata a farmakan da aka kai a Middle Shabelle, da Galgadud da lardin Mudug na arewa ta tsakiyar Somalia.

Sama da 'yan ta'adda 59 da sojoji huɗu sun mutu a farmakan soji da aka kai a Somalia a watan Oktoba, kuma a tsakanin 12 ga Nuwamba da 3 ga Disamba an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 50, wanda ya kawo adadin zuwa 304.

Rashin tsaro na addabar kasar

Tun shekarar 2022 sojojin gwamnati, da 'yan bindiga da ƙawayensu na ƙasa da ƙasa na kai farmakai a kai a kai kan 'yan ta'addan.

Tsawon shekaru Somalia na fama da matsalar tsaro, inda ƙungiyoyin ta'adda na Al-Shabab da Daesh ISIS ke yin babbar barazana.

Tun 2007, Al-Shabab ke yaƙi da gwamnatin Somalia da Dakarun Tarayyar Afirka a Somalia (ATMIS) - wata runduna ta musamman ƙarkashin Tarayyar Afirka da ta samu halasci daga Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kungiyar ta'addar ta ƙara yawan kai hare-hare tun bayan da shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya ayyana "yaƙar 'yan ta'addar baki ɗaya".

ɗ

TRT Afrika