Sojojin sun kashe 'yan ta'addan biyu a yayin musayar wutar. Hoto/Forces Armées Nigériennes

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan ayarin motocin Rundunar Sojin Jamhuriyyar Nijar.

Lamarin ya faru ne a yayin da kwambar motocin ke kan hanyar zuwa wani aiki a tsakanin Torodi da Makalondi da ke yankin Tillaberi.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta Nijar ta fitar, an yi musayar wuta mai karfi tsakanin dakarun Nijar din da ‘yan ta’addan.

Daga bangaren sojojin, mutum biyar sun rasa ransu wadanda suka kunshi jandarma daya da kuma farar hula hudu.

Sa’annan kuma mutum 19 sun samu rauni wadanda suka hada da jandarma bakwai da sojoji biyar da farar hula bakwai.

Sojojin kuma sun bayyana cewa akwai manyan motocinsu hudu da ‘yan ta’addan suka lalata a yayin ba-ta-kashin.

A sanarwar wadda shugaban sojin kasa na Nijar Abdou Sidikou Issa ya saka wa hannu, sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu sa’annan suka kwato babura biyu daga wurinsu.

Sa’annan sojojin sun kwace bindiga kirar AK47 guda biyu da wata ‘yar karamar radiyo.

Kwato harsasai

Rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar din na cewa a ranar Juma’a dakarun kasar sun samu nasarar kwato harsasai wadanda ake zargin za a kai wa ‘yan ta’addan ISWAP.

Lamarin ya faru ne a lokacin da dakarun Nijar din da ke a N’Gagam suka bi wata mota kirar Toyota Hilux inda aka samu akwatuna 19 makare da harsasai a ciki, kamar yadda jaridar Air info ta Nijar ta ruwaito.

Rahotanni sun ce bayan bude akwatunan, an samu jimilar harsasai 23,430. Haka kuma akwai mutum biyu wadanda suke a cikin motar an kama su.

TRT Afrika