Ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigar suka sace ɗalibai sama da ɗari a ƙauyen Kuriga da ke Kaduna. / Hoto: Reuters

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kashe wasu ƴan ta’adda a Kaduna da ke arewacin Nijeriya.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa sojojin sun kashe ƴan ta’addan waɗanda suka shahara wurin amfani da babura domin kai hare-hare bayan samun bayanan sirri a kansu ta hanyar yi musu kwanton-ɓauna.

Rundunar ta ce ta rutsa ƴan ta’addan ne a kusa da ƙauyen Kidandan da ke Ƙaramar Hukumar Giwa inda suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu.

Rundunar ta ce ƴan ta’addan sun tsaya yada zango ne domin gyaran baburan da suke amfani da su wurin kai hare-hare a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sojojin sun ce baya ga kashe ƴan ta’addan uku, sun samu nasarar ƙwato bindigar Ak 47 ɗaya da babura huɗu da wayar oba-oba ɗaya samfarin Motorola.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ake fama da hare-haren ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigar suka sace ɗalibai sama da ɗari a ƙauyen Kuriga, sai dai daga baya an sako daliban.

Haka kuma ƴan bindigar sun sace aƙalla mutum 87 a Ƙaramar Hukumar Kajuru da ke jihar ta Kaduna.

TRT Afrika