Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ce ya yi kokarin kawo karshen zaman sojojin Faransa a kasarsa. / Hoto: Reuters

Faransa da Senegal sun sun yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai tsara ficewar sojojin Faransa daga kasar da ke yammacin Afirka nan da karshen shekara ta 2025, kamar yadda ƙasashen biyu suka tabbatar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, kasashen biyu na da niyyar yin hadin gwiwa a fannin tsaro da ke la'akari da muhimman tsare-tsare na dukkan bangarorin.

Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ce ya yi kokarin kawo karshen zaman sojojin Faransa a kasarsa.

Faye ya shaida wa jaridar Le Monde a watan Nuwamba cewa, "Nan ba da jimawa ba Senegal za ta kasance ba ta da sojin Faransa ko ɗaya."

“Buƙatar ficewa”

Sojojin Faransa sun ci gaba da zama a Senegal tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, musamman domin horo da ayyukan tsaro a yankin. A halin yanzu akwai sojojin Faransa 350 a kasar.

Kalaman Faye sun kasance sanarwa ta farko daga gwamnatin Senegal da ta bukaci ficewar sojojin Faransa.

Firaminista Ousmane Sonko ya soki kasancewar sojojin Faransa a cikin watan Mayu lokacin da ya nuna shakku kan wajibcin samun kasa mai cin gashin kanta.

Faransa dai ta kawo karshen zaman soji a kasar Chadi a watan da ya gabata, inda ta bar sansaninta na karshe kwana guda gabanin wa'adin da mahukuntan Chadin suka sanya.

Tasirin sojojin Faransa a ƙasashen Afirka ya yi matuƙar raguwa tun bayan da ƙasashe da dama a nahiyar suka sallami sojojin daga ƙasashen nasu.

AA