Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da gagarumin bututun danyen man fetur wanda zai rika kai fetur zuwa Jamhuriyar Benin, kamar yadda gidan talbijin na kasar ya sanar ranar Laraba.
Bututun danyen man fetur din mai tsawon kusan kilomita 2,000 zai bai wa Nijar damar sayar da fetur ga kasashen duniya a karon farko ta tashar jiragen ruwa ta Seme da ke Benin.
An kaddamar da bututun man fetur din ne a garin Agadem na jihar Diffa, mai nisan fiye da kilomita 1,700 daga Yamai.
Firaiministan kasar Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce za a yi amfani da kudin da aka hako fetur din wajen "tabbatar da ci-gaban kasarmu mai cin gashin kanta".
An rufe iyakar Nijar da Benin bayan takunkumin da kungiyar ECOWAS ta sanya wa kasar sakamakon juyin mukin da sojoji suka yi a watan Yulin da ya gabata.
Ministocin Makamashin daga Mali da Burkina Faso -- kasashen da ke karkashin mulkin soji kuma suke goyon bayan Nijar -- sun halarci bikin kaddamar da batutun danyen man fetur din.
Tun a shekarar 2022 aka yi niyyar bude bututun man amma aka fasa sakamakon barkewar annobar korona, a cewar wadanda ke kula da shirin a hirarsu da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kamfanin fetur na China National Petroleum Corporation (CNPC) ne yake daukar nauyin hakar man na Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin Nijar ta ce an kashe kimanin $6 b wajen hakar man fetur din, ciki har da $4 b da aka kashe wajen yin nazari kan gano fetur da kuma $2.3 b da aka kashe wajen gina bututun man.
Ta ce wannan shiri zai ba ta damar hako karin gangar mai 110,000 a kowacce rana, tana mai karawa da cewa nan da shekarar 2026 tana sa ran hako ganganr mai 200,000 kowacce rana.