Sojojin Nijar shida da ‘yan ta’adda 10 ne suka mutu a wata fafatawa da suka yi a yammacin kasar, a cewar hukumomi.
Wasu da ake zargin masu tayar da kayar baya ne a kan babura suka yi wa sojojin kwanton-bauna a kusa da garin Sanam a ranar Lahadi, a cewar wata sanarwa da rundunar tsaron kasar ta fitar.
Sanam yana yankin Tillaberi da ya hada iyakar Nijar da kasar Mali da Burkina Faso, yankunan da ke yawan fama da hare-haren 'yan bindiga.
A ranar 9 ga watan Agusta, an kashe sojoji biyar a wani hari da aka kai a yankin, a cewar gwamnatin sojan da ta hambarar da Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.
Jagoran juyin mulkin na Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya kafa hujjar cewa sun kifar da gwamnatin Bazoum sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar.