Shugabannin Afirka da dama sun ce sun kaɗu da jin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na Iran 

Shugabannin ƙasashen Afirka da dama sun bi sahun takwarorinsu na duniya wajen aikewa da saƙonnin ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Iran kan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi, bayan wani haɗarin jirgin sama.

A safiyar Litinin ne hukumomin Iran suka tabbatar da mutuwar Raisi, bayan an shafe sa'o'i ana ƙoƙarin gano inda jirginsu ya faɗi a kusa da iyakar ƙasar da Azerbaijan.

Hatsarin jirgin ya faru ne ranar Lahadi, bayan Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar da gwamnan Azerbaijan ta Gabas a Iran da wasu jami'ai da masu tsaron lafiyar shugaban sun baro ƙasar Azerbaijan mai maƙotaka.

A saƙonsa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar Iran kan rashin shugabannin.

Shi ma Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, wanda a baya-bayan nan ya gayyaci Iran ta shiga ƙungiyar BRICK, ya nuna jimami kan rasuwar Ebrahim Raisi da sauran mutanen da hatsarin ya rutsa da su.

"Wannan wani tashin hankali ne mai girma, wanda ba a taɓa tunaninsa ba wanda kuma ya yi sanadin rasuwar babban jagora na ƙasar da Afirka ta Kudu take jin daɗin alaƙar diflomasiyya da ita," a cewar Shugaba Ramaphosa.

Ƙasar Aljeriya na daga ƙasashen da suka tura saƙon alhini bisa rasuwar Ebrahim Raisi. A saƙon da ya gwamnatin ƙasar ta wallafa a shafin X, ta ambato Shugaba Abdelmajid Tebboune yana miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan mutuwar Shugaba Raisi.

Shugaban Masar Abdul Fatah al Sisi ma ya fitar da sanarwa inda ya ce “Shugaban Jamhuriyar Larabawa ta Masar na miƙa tsantsar ta’aziyya da jimami ga ‘yan uwa jama’ar Iran.” Ya kuma ce Jumhuriyar Larabawan Masar na tare da shugabanni da jama’ar Iran a wannan mawuyacin hali.

William Ruto Shugaban Kenya ya ce mutuwar Raisi da Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Abdollahian da tawagarsu, babban abin tashin hankali ne. "Ina so in miƙa saƙon ta'aziyyata ga goyon baya da kasancewa tare da mutanen Iran a wannan lokaci mai wahala," a cewar William Ruto.

Ita ma Shugabar Tanzamia Samia Sululhu Tanzaniya ta aike da ta'aziyya kan rashin Shugaba Raisi da sauran mutane da hatsarin jirgin ya rutsa da su.

Ta ce "A madadin gwamnati da jama'ar Tanzaniya, ina miƙa ta'aziyyarmu ga gwamnati da jama'ar Iran kan mutuwar Mai Girma Ebrahim Raisi, Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Muna tare da ku a cikin jimamin rashin shugabanku kuma muna muku fatan samun ƙarfin gwiwa da nutsuwa a wannan lokaci mai wahala," kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Gwamnatin Maroko ita ma ta aike da nata saƙon na ta'aziyya kan rasuwar shuagaban na Iran.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar aka kuma wallafa ta a shafin X, ta ce "Masarautar Maroko tana miƙa ta'aziyyarta ga mutanen iran da iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma."

TRT Afrika da abokan hulda