Shugabannin Afirka da ke taro a birnin Accra na kasar Ghana sun yi kira ga kasashen turai su biya diyya kan cinikin bayi da kakaninsu suka yi a zamanin mulkin-mallaka.
Sun bayyana cewa har yanzu al'ummar Afirka na fama da tabon musgunawa da kuma take hakkin da aka yi wa kakaninsu lokacin cinikin bayani.
Mahalarta taron, wanda shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo yake jagoranta, sun bayyana irin zallan zalunci da rashin imani da masu cinikin bayi suka yi wa 'yan Afirka, suna masu cewa matakin ya zubar da kima da darajar 'yan Afirka.
Da yake jawabin bude taron na kwanaki hudu, Shugaba Akufo-Addo ya ce "cinikin bayi shi ne zamani na dabbanci da rashin tausayi da 'yan Afirka suka fuskata."
"Cinikin bayin ya kawo koma-baya ga Afirka ta fuskar tattalin arziki da al'adu da yanayin tunani. Ba za a iya kimanta illar da hakan ya yi ba, amma ya kamata a sani cewa al'ummar Afirka ta yi gagarumar asara a wancan zamanin kuma har yanzu wannan asara tana bibyarmu," in ji shi.
Tun tuni ya kamata a biya diyya kan wannan mugunta da aka yi wa 'yan Afirka, a cewar shugaban na Ghana.
A jawabin da aka karanta a madadinsa, shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya ce Afirka ta kwashe tsawon lokaci tana fama da illolin da cinikin bayi ya haifar mata.
A nasa bangaren, shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, wanda aka wakilce shi, ya jaddada goyon bayan kasarsa wajne ganin an dauki matakin karbo diyya kan cinikin bayi.
Bayanai sun nuna cewa an kwashi bayi kimanin miliyan 12 ta Kogin Atlantika zuwa Amurka a karni na 16 zuwa 19 inda aka tilasta musu yin ayyukan bauta da wulakanta su.