A 2019 Kais Saied ya hau kujerar shugaban kasa a karon farko. / Photo: Reuters

Shugaban Ƙasar Tunisia Kais Saied na kan hanyar lashe zaɓen shugaban ƙasar da kashi 89.2 duk da ƙarancin fitar masu kaɗa ƙuri'a rumfunan zaɓe, kamar yadda sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi bayan kammala zaɓen ta bayyana.

Ana sa ran Saied mai shekaru 66 zai lashe zaɓen da gagarumar nasara, ya yi fintinkau ga abokan hamayyarsa - Ayachi Zammel da aka ɗaure a kurkuku da zai samu kashi 6.9 na ƙuri'un, da Zouhai Maghzaoul, da zai samu kashi 3.9, in ji ƙungiyar Sigma Conseili mai zaman kanta da ke sanya idanu kan zaɓe.

Shekaru uku bayan Saied ya lashe zaɓe, ƙungiyoyin farar-hula suka fara fargabar cewar idan ya sake lashe zaɓen zai tsawaita wa'adinsa a kan mulkin ƙasar, wadda ita kaɗai ta koma turbar dimokuraɗiyya tun bayan juyin juya halin ƙasashen Larabawa.

Bayan kawar da Zine El Abidine Ben Ali a 2011 bayan wanda ya kwashe lokaci mai tsawo yana mulki, Tunisia ta yi alfaharin zama ƙasar da aka fara boren da ya ƙalubalanci mulkin kama-karya a yankin.

Halascin ƙuri'u

Hukumar zaɓen Tunisia, ISIEC, ta ce akwai kimanin mutane miliyan 9.7 da suka cancanci jefa ƙuri'a a ƙasar, wadda ke da yawan mutane miliyan 12.

Kashi 27.7 na masu jefa ƙuri'a ne kawai suka fita rumfunan zaɓe, in ji hukumar.

Fiye da kashi 58 maza, da kashi 65 tsakanin masu shekaru 35 da 60.

"Halascin ƙuri'un ya samu cikas inda 'yan takara da suka gaza danne Saied, aka dinga bin tsarin danne su," in ji Hatem Nafti, wani mai sharhi kan lamuran siyasa kuma marubucin littafin kan mulkin kama-karya na shugaban da ke shirin fitowa a nan gaba.

'Mayaudara da maƙiya'

"Saied ya yi alƙawarin raba ƙasar Tinusia da mayaudara da maƙiyanta," in ji Nafti. "Zai yi amfani da sake lashe zaɓe ya dinga gallaza wa mutane."

Hukumar zaɓe ta ISIE ta hana mutane 14 tsayawa takara, tana mai cewa ba su samu amincewar da ta kamata ba, da ma wasu matsaloli.

A ranar Litinin ɗin nan hukumar za ta sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen.

Fita zaɓe a wannan shekarar ne mafi ƙaranci tun bayan juyin juya halin ƙasar a 2011, idan aka kwatanta da na shekarar 2019 da ya kasance kashi 45.

'Babu adadin kuri'u mafi ƙaranci'

"Tabbas halascin dikomuraɗiyya" na ƙuri'un na da rauni, amma babu mafi ƙarancin adadi da mutum zai samu don lashe zaɓe, in ji mai nazari kan siyarar arewacin Afirka Perre Vermeren. "Mafi yawancin 'yan ƙasar Tunisia sun zuba ido suna kallo ne".

Hosni Abidi, mai shekaru 40, ya ce ya ji tsoron tafka maguɗi bayan da hukumar zaɓe ta kori wasu ƙungiyoyi biyu masu sanya idanu daga bin diddigin zaɓukan.

"Ba na son mutane su yi zaɓi a madadina," in ji shi.

"Ina son na zaɓi ɗan takarar da nake so da kaina."

'Sun gamsu da manufofin Saied'

Saied ya jefa ƙuri'a tare da matarsa a unguwar Ennasr ta masu kuɗ, da ke yammacin birnin Tunis da safiya.

Jim kaɗan bayan bayyana kammala jefa ƙuri'a magoya baya sun fita kan tituna suna murnar tsammanin nasara.

"Na gamsu da tunani da salon siyasarsa," in ji Oumayma Dhouib, mai shekaru 25.

Karɓar mulki da Saied ya yi a 2021 ya ba shi damar sauya kundin tsarin mulki tare da murƙushe 'yan adawa, wanda hakan ya janyo masa suka daga ciki da wajen ƙasar.

Zammel a kurkuku tsawon shekaru 14

Ƙungiyar Kare Hakkokin Ɗan'Adam ta Human Rights Watch da ke New York ta ce "An kama tare da tsare mutane 170 a Tunisia saboda dalilai na siyasa."

Babban mai ƙalubalantarsa, Zammel, ya fuskanci ɗaurin shekaru 14 a gidan kurkuku bisa zarginsa da ƙirƙirar sanya hannun amincewar jama'a don samun damar tsayawa takara.

Sauran waɗanda aka ɗaure sun haɗa da Rached Ghannouchi, shugaban jam'iyyar adawa ta Ennahdha, wadda ta mamaye fagen siyasa bayan juyin juya halin ƙasar.

Kazalika an ɗaure Abir Moussi, shugaban jam'iyyar FDP, wadda masu suka suke zarga da dawo da gwamnatin da aka kifar a 2011.

Zamanin sake gina ƙasa

A jawabinsa na ranar Alhamis, Saied ya yi kira da "A fita sosai don jefa ƙuri'a" don kawo sabon zamanin gina ƙasa".

Ya bayyana "daɗaɗɗen yaƙin haɗin baki da wasu na cikin gida da ƙasashen waje", yana mai sukarsu da "shiga hukumomin gwamnati da kutse cikin ayyuka da dama a zamanin mulkinsa."

Ƙungiyar Sanya Idanu Kan Rikici ta Ƙasa da Ƙasa ta ce a yayin da Saies "ke samun goyon baya sosai a tsakanin talakawa, ana sukarsa da gaza warware matsalolin tattalin arziki da ke damun ƙasar."

"Da yawa na tsoron sabon wa'adin mulki ga Saied ba tattalin arziki da zamantakewa zai ci gaba da lalatawa ba, zai kuma hanzarta kama-karyar gwamnatin."

TRT Afrika