Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya buƙaci Faransa ta rufe sansanonin sojinta a ƙasar a daidai lokacin da ƙasar za ta yi jimamin cika shekara 80 da faruwar wani mummunan kisa da sojojin Faransa suka yi wa dakarun ƙasar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da cewa sojojin ƙasarsa sun aikata “kisan kiyashi” ga sojojin Senegal a 1994, kamar yadda Faye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Alhamis.
Faye ya yaba da kalaman na Macron amma ya ce barin sansanonin Faransa a cikin ƙasar bai dace da ikon kasa ba.
"Senegal kasa ce mai cin gashin kanta, kuma tsarin kasar bai yarda da kasancewar sansanonin soji ƙasashen waje a cikin ƙasa mai cin-gashin-kanta ba," in ji Faye a wata hira da aka yi da shi a Fadar Shugaban Ƙasa.
Korar dakarun Faransa
Faye ya hau kan karagar mulki a zaben da aka yi a watan Maris inda ya yi alkawarin tabbatar da ikon Senegal da kuma kawo karshen dogaro ga kasashen ketare. Sai dai ya ci gaba da cewa dokar ba dauke wa Faransa hakan ba.
Wasu kasashe masu amfani da harshen Faransanci da dama a yammaci da tsakiyar Afirka, da suka hada da Mali, Burkina Faso da Nijar, inda sojoji ke rike da madafun iko, sun kori sojojin Faransa tare da komawa ga wasu abokan hulda domin taimakon tsaro a madadin Faransan.
Wasu majiyoyin gwamnatin Faransa guda biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a wannan shekara cewa kasar na neman rage yawan sojojinta a Afirka daga dakaru 350 zuwa 100 a Senegal da Gabon da kuma 300 a Chadi daga 1,000 da 100 a Cote d'Ivoire daga 600.
Faye ya ce "Faransa ta kasance muhimmiyar abokiyar kawance ga Senegal don zuba jari ga Senegal da kasancewar kamfanonin Faransa da ma 'yan kasar Faransa da ke Senegal."
Macron ya amince da kisan gillar sojoji
Shugaban kasar Senegal ya ce ya samu wasika daga Macron inda ya amince da laifin Faransa a kisan kiyashin da aka yi a Thiaroye a lokacin Yakin Duniya na Biyu a ranar 1 ga Disamba, 1944.
An dade ana kai ruwa rana tsakanin Paris da Dakar a kan wannan danyen aikin.
A watan Nuwamban 1944, an mayar da kusan sojojin Afirka 1,600 da suka yi yaƙi don Faransa kuma Jamus ta mayar da su fursunonin yaƙi, zuwa Dakar, a cewar wani masanin tarihin Faransa Armelle Mabon.
Jim kadan bayan isa sansanin Thiaroye da ke wajen birnin Dakar, sun yi zanga-zangar adawa da jinkirin biyansu albashi, inda wasu suka ƙi komawa kasashensu ba tare da biyansu hakkokinsu ba.
Sai sojojin Faransa suka bude wuta kan masu zanga-zangar, inda suka kashe akalla soji 35, ko da yake masana tarihi sun ce adadin ya zarta haka.