Nana Akufo-Addo ya caccaki shugabannin da ke yin ta-zarce./Hoto: Reuters

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dauki mataki kan shugabannin da ke sauya kundin tsarin mulkin kasashensu da zummar ci gaba da zama a kan mulki.

Akufo-Addo ya ce irin wannan mataki ne yake janyo al'uumar kasashen su harzuka abin da kan "zama silar juyin mulki."

Shugaban kasar ta Ghana ya bayyana haka ne ranar Juma'a a garin Winneba da ke kudancin kasar, inda 'yan majalisar dokokin kungiyar ECOWAS suke gudanar da taro.

'Yan majalisar dokokin nan kasashen kungiyar ECOWAS suna taro ne kan "Kalubalen da ke da alaka da saye-sauyen kundin tsarin mulki da wa'adin shugabannin kasashe a Yammacin Afirka – Rawar da Majalisar Dokokin ECOWAS za ta taka."

Akufo-Addo ya ce tattaunawa game da wa'adin mulkin shugabannin kasashe zai sa al'ummomi su ki yanke kauna game da mulkin dimokuradiyya.

Ya caccaki shugabannin da ke fakewa da "tsarin doka" wajen "jirkita kundin tsarin mulki da kuma amfani da hukumomin gwamnati domin ci gaba da zama a kan mulki."

Akufo-Addo ya yi wannan tsokaci ne bayan shugabannin kasashe da dama da ke kungiyar ECOWAS da ma wadanda ba sa cikinta, sun sauya kundin tsarin mulkinsu domin samun damar yin ta-zarce.

Gabon, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Uganda da Equatorial Guinea na cikin kasashen da shugabanninsu suka sauya kundin tsarib mulkinsu domin sake tsayawa takara bayan wa'adinsu ya kare.

A baya shugabannin ECOWAS sun yi yunkurin takaita wa'adin shugabannin kasashe zuwa biyu, amma ba a amince da wannan shawara ba. Sau uku ana yin fatali da irin wannan shawara, ciki har da wadda aka ki amincewa da ita a 2015.

TRT Afrika