Umarnin na zuwa ne bayan ECOWAS ta yi zama a kwanakin baya inda ta ce a cire takunkuman. / Hoto: Getty Images

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni a buɗe iyakokin ƙasar da na Nijar nan-take.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duka sauran takunkuman da Nijeriyar ta saka wa Nijar.

Shugaban ya bayar da umarni kan a ɗage waɗannan takunkuman da aka saka wa Nijar nan take: -

1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakanin Nijeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.

2- Dakatar da duka cinikayya tsakanin Nijeriya da Nijar, da dakatar da duka ayyukan da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.

3- Riƙe ƙadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.

4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.

5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu

Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea.

Wannan na zuwa ne bayan ECOWAS ta cire takunkuman da ta saka wa Nijar a kwanakin baya.

An shafe lokaci mai tsawo ana dambarwa tsakanin ECOWAS da Nijar da Burkina Faso da Mali, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Dambarwar ta samo asali ne tun bayan da sojojin da ke mulkin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki a 2023 wanda hakan ya ja ECOWAS ta saka wa Nijar ɗin takunkumi.

TRT Afrika