Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga Musulmai su rungumi ilimin boko saboda kimar da yake bayarwa.
Ya yi wannan kira ne yayin da ya ke jawabi ga al’ummar Musulmai a wajen taron bikin babbar Sallah ta kasa na bana, a dandalin Independence Square da ke Accra.
Ya ce kasar za ta bai wa 'ya'yan Musulmai dama don cin moriyar da ilimin boko ke bayarwa a rayuwar dan Adam.
''Ina so na kara muku kwarin gwiwa cewa ku yi rungumi manufofinmu na ci-gaba a fannin ilimi don tarbiyyantar da ‘ya’yanku maza da mata,” in ji shi.
Ba da Ilimi ga duk wani dan Musulmi na daga cikin abubuwan da addinin Musulunci ya gindaya, a cewar Shugaba Akufo-Addo.
"Ina sane da cewa ayoyin da aka fara saukar wa Annabi Muhammad (SAW), suna cewa, ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta...ka yi karatu, kuma ubangijinka shi ne mafi falala.
Ya koyar da mutum da alkalami. Kuma ya sanar da mutum abin da bai sani ba," kamar yadda shugaban ya ambato Allah yana cewa a cikin Alkur'ani.
Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi nuni da cewa ta hanyar ilimi, an baiwa Musulman Ghana da damar kai wa ga kololuwar ci-gaban kowanne fanni na rayuwarsu.
Ya kara da cewa ''akwai adadi mai yawa na irin wadannan mutane da suka yi aiki a bangarori daban-daban kuma sun ci gaba da ba da kwarewarsu don ci-gaban al'umma''.
Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta bar kowa ba, ciki har da al’ummar Musulmai, wajen rabon kayayyakin da ake bukata wajen gina ma’aikatu masu inganci da dai sauransu.