An katse hanyoyin intanet a Dakar babban birnin Senegal da kuma sauran sassan ƙasar a daidai lokacin da ƴan majalisa a ƙasar ke shiri tafka muhawara kan wani kudiri da zai iya ƙara wa’adin mulkin Shugaba Macky Sall gaba da 2 ga watan Afrilu, wanda lokacin ne ya kamata ya bar ofis.
Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki Na Zamani a wata sanarwa da ta fitr ta ce ta yanke intanet ɗin ne “sakamakon watsa labaran ƙiyayya waɗanda ake watsawa a shafukan sada zumunta domin barazana ga zaman lafiyar jama’a.
A ranar Lahadi ne Ƙungiyar Tarayyar Afirka AU ta ce akwai buƙatar ƙasar Senegal ta yi gaggawar gudanar da zaɓe.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ƙasar Macky Sall ya sanar da ɗaga zaɓen ƙasar wanda aka yi niyyar gudanarwa 25 ga watan Fabrairu.
Wannan ne karo na farko da Senegal ke jinkirta zaɓen shugaban ƙasa, haka kuma sanarwar da Sall ya bayar a ranar Asabar ta jefa ƙasar cikin ruɗani inda yan adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka yi ta mayar da zafafan martani.
“Akwai buƙatar Senegal ta yi gaggawar gudanar da zaɓe cikin kwaciyar hankali da haɗin kai,” kamar yadda shugaban na AU Moussa Faki Mahamat ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da dare.
Arangama a Dakar
Ana sa ran ƴan majalisa a Senegal za su tafka muhawara a ranar Litinin, domin tattaunawa kan ko a yi zaɓe a ranar 25 ga watan Agusta da kuma batun Sall ya ci gaba da zama a kan mulki har sai an rantsar da magajinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
A ranar Lahadi, an yi arangama a Dakar tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga kan batun ɗaga wannan zaɓen na shugaban ƙasa. Ƴan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar.
Sai masu zanga-zangar suka mayar da martani ta hanyar jefa duwatsu ga jami’an tsaron, kamar yadda bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna.
Dakatar da tashar talabijin
A ɗayan ɓangaren kuwa hukumomi sun dakatar da wata kafar watsa labarai ta talabijin a ƙasar inda ake zarginta da harzuƙa jama’a.
Ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ce ta dakatar da Walf TV, mallakar Wal Fadjri.
Ousseynou Dieng, daraktan watsa labarai na ƙasar ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai domin dakatar da gidan talabijin ɗin na wucin-gadi.