Sauyin yanayi ne ya ta'azzara mummunar ambaliyar ruwa a Yammaci da Tsakiyar Afirka

Sauyin yanayi ne ya ta'azzara mummunar ambaliyar ruwa a Yammaci da Tsakiyar Afirka

Tawagar masana kimiyya ta ƙasa da ƙasa ta yi gargaɗi cewa za a iya smaun irin wannan mamakon ruwan sama duk shekara.
Mutane yayin taimaka wa wani tsoho da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Maiduguri arewacin Nijeriya. / Hoto: AFP

Mamakon ruwan sama da ya janyo ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyar rasa rayuka a Kamaru, Chadi, Nijeriya, Nijar da Sudan a watannin baya-bayan nan ya ta'azzara sakamakon sauyin yanayi da ɗan'adam ke janyo wa, in ji wasu masana kimiyya a ranar Laraba.

Ɗumamar yanayi ta sanya ruwan saman da aka samu a wannan shekarar ƙaruwa da kashi biya zuwa 20 a Nijar da gabar Tafkin Chadi, in ji WWW, ƙungiyar masana kimiyya da ke nazari kan alaƙar sauyin yanayi da halin da duniya ke ciki.

Ƙungiyar ta ce irin wannan mamakon ruwan sama na iya afkuwa kowace shekara idan ɗumamar ta ci gaba.

"Mamakon ruwan sama a lokacin zafi ya zama ruwan dare a Sudan, Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chadi," in ji Izidine Pinto, mai bincike a cibiyar bincike kan yanayi ta 'Royal Netherlands Meteorological Institute'.

Mutum miliyan guda sun rasa matsugunansu

Ambaliyar ruwa a wannan shekarar ta kashe mutane 1,500 tare da tsugunar da sama da miliyan guda a Yammaci da Tsakiyar Afirka, kamar yadda Hukumar MDD ta OCHA ta bayyana. Ruwan saman da aka samu ya karya madatsun ruwa a Nijeriya da Sudan.

Idan ɗumamar yanayi ta kai digiri biyu a ma'aunin selishiyos, wanda zai iya faruwa nan da farkon 2050, to ana sa ran irin wannan mamakon ruwan saman zai dinga faruwa duk shekara a yankunan, in ji WWA, inda suka yi kira da a zuba jari wajen ɗaukar matakan ƙarfafa madatsun ruwa.

"Afirka ta bayar da gudunmawa 'yar kaɗan ga samuwar iskar carbon da ke gurɓata yanayi, amma kuma ta fi fama da illa daga tasirin ɗumamar yanayin," in ji Joyce Kimutai, mai bincike a Cibiyar Nazarin Muhalli a Imperial College London.

Ta ce a wajen taron sauyin yanayi na bana na COP29 a watan Nuwamba ana sa ran manyan ƙasashe za su taimaka da kuɗaɗe don yaƙi da matsalar.

TRT Afrika