Rwanda

Shekara 29 kenan tun bayan kisan kare dangin Rwanda inda aka yi kiyasin mutum 800,000 mafi yawa 'yan kabilar Tutsi ne aka kashe a cikin kwana 100.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka AU, suna tuna wa duniya cewa ya kamata a koyi hakuri da juna da ci gaba da samar da mutuntaka da tsaro da adalci da bai wa kowa 'yancinsa na dan adam.

“Ka da mu sake bari a yi wani rikici da zai jawo kisan kare dangi a nahiyar Afirka," a cewar Ambasada Bankole Adeoye, Kwamishinan Harkokin Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU.

Sai dai kuma a yau, Rwanda ta samu ci gaba sosai tun bayan mummunan kisan kare dangin, wanda yana daga cikin mafi munin abubuwan da suka faru a karni na 20.

Kisan kare dangin ya yi sanadin da 'yan kabilar Hutu masu tsattsauran ra'ayi suka kashe 'yan kabilar Tutsi da yawa da kuma tsirarun 'yan kabilar Hutu masu matsakaicin ra'ayi.

Kasar ta haramta amfani da harshen da ke nuna wariya ko kabilanci a kasar.

Tsawon rayuwar da ake sa ran 'yan Rwanda za su iya yi ya haura shekara 60, wanda ya nunka yadda yake a shekarar 1994.

Haka kuma an samu raguwa matuka a yawan mace-macen yara 'yan kasa da shekara biyar a cikin shekara 20 da suka wuce.

A watan Yunin 2002, Rwanda ta fara wani muhimmin shiri na samar da waraka da yin sulhu ta wani tsari na shari'a da ake kira Gacaca court.

“Ka da mu sake bari a yi wani rikici da zai jawo kisan kare dangi a nahiyar Afirka."

Ambasada Bankole Adeoye, Kwamishinan Harkokin Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU

Cikin shekara 10, kotuna a kasae sun yi shari'u kusan na mutum miliyan biyu da ake zargin su da kisan kare dangi.

Sannan mata su ne kashi 61.3% na majalisar dokokin Rwandan, lamarin da ya sa kasar ta shiga sahun kasashen da suka fi yawan mata a majalisa a fadin duniya.

Kazalika Rwanda ta zamo daya daga cikin kasashe kalilan na Afirka da suke samar da rigakafi, inda har kamfanin samar da rigakafi na Jamus Biontech ya kafa reshe a kasar.

Harkar yawon bude ido ta zama babbar hanyar samar wa da kasar kudaden shiga, inda yawan gwaggwan birrai da Rwanda ke da su ya sa hakan ne jan hankalin kasashen duniya.

Haka kuma Rwanda ta samar da tsarin kiwon lafiya na duniya mai suna has 'Mutuelle de Santé’ kuma tana cikin kasashen Afirka na farko da suka kaddamar da wani tsari na samar da jirgi maras matuki.

Kasar ta kuma rungumi harkar fasaha da kirkire-kirkire inda ta samar da abubuwa da yawa na basirar na'ura AI don taimaka wa 'yan Rwanda samun saukin ganawa da kwararru a fannin lafiya.

A shekarar 2008, Rwanda ta haramta amfani da ledoji, kuma Hukumar Kula da Muhalli ta MDD ta ce Kigali, babban birnin Rwanda na daga cikin biranen Afirka mafiya tsafta.

MDD ta taba ayyana babban birnin Rwanda a matsayin daya daga cikin mafiya tsafta a Afirka saboda matakin kasar na hana amfani da leda/Hoto AP

A bangaren wasanni kuwa, Rwanda ta zuba kudi sosai ta hadin gwiwa da manyan kungiyoyin wasa na duniya irin su Arsenal da PSG.

Ta kuma zuba jari sosai a gasar wasannin kwallon kwando da na tseren kekuna.

A yau, matasan da aka haifa bayan kisan kare dangin, suna kallon kansu ne a matsayin mutane masu burin gaba ta fi baya kyau, wadanda suke bayyana kansu a matsayin 'yan Rwanda ba wai alakanta kansu da wata kabilar kasar ba.

TRT Afrika