Paul Rusesabagina, wanda ya fito a matsayin jarumi a fim din "Hotel Rwanda" da aka yi a kan kisan kiyashi na shekarar 1994, ya isa Qatar bayan an sake shi daga gidan yari a makon da ya gabata a Rwanda, in ji mai magana da yawun gwamnatin Rwanda ranar Talata.
An yanke wa Rusesabagina, mazaunin din-din-din a kasar Amurka, hukuncin daurin shekara 25 a watan Satumban shekarar 2021 kan dangantakarsa da wata kungiyar mai reshen dake dauke da makami dake hamayya da Shugaba Paul Kagame.
An sake shi ne ranar Juma’a bayan an rage tsawon daurin da aka yi masa bayan tattaunawa ta watanni tsakanin Washington da Kigali.
Mutumin mai shekara 68 da yake aikin otel a da ya sauka a Doha ranar Litinin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Rwanda, Yolande Makolo, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai ta Reuters.
Fim din "Hotel Rwanda" ya bayyana nasarar da Rusesabagina ya yi wajen ceto rayukan mutum sama da 1,000 a lokacin da aka yi kisan kiyashi na shekarar 1994 ta hanyar ba su mafaka acikin otel din da yaka kula da shi a birnin Kigali.
Kara gyara dangantakar Rwanda da Amurka
A lokacin da ake shari’arsa, Rusesabagina ya yarda cewa shi yana da mukami na shugaba a wata kungiyar ‘yan hamayya, amma ya ce ba shi da hannu a cikin hare-haren da da reshen yaki na kungiyar ya kai a Rwanda.
Masu shari’ar sun ce ba za a iya raba tsakanin rassan kungiyar guda biyu ba.
A wata wasikar da ya aika wa Kagame a farkon wannan watan, Rusesabagina ya ce idana ka yafe masa kuma aka sake shi, zai bar siyasa kuma kare rayuwarsa a Amurka "yana mai tunani ".
Daurin da aka yi wa Rusesabagina ya rage dankon zumuncin da ke tsakanin Amurka da Rwanda tare da zargin da Amurka ta yi wadda Rwanda ta musanta cewar Rwanda ta tura sojojinta Kongo mai makwabtak,a kuma tana bai daura wa ‘yan tawaye gindi a kasar.
Rwanda ta ce sake Rusesabagina sakamako ne na son gyara dangantaka tsakanin Amurka da Rwanda.