Daga Coletta Wanjohi
Isar wasu kwantenoni biyu wadanda ake kira BioNtainers kasar Rwanda, za su zama wata babbar alama ta dogaro da kai ga nahiyar Afirka ta fannin samar da rigakafi.
Bukatar da ake da ita ta ‘BioNtainers’ – wadanda wasu 'yan kwarya-kwaryan kamfanoni ne sun fito karara da irin matsalolin da nahiyar ke fuskanta ta fuskar samar da magungunan da za su kare rayuka sakamakon karancin kayan aiki.
Sai dai ana sa ran nahiyar wadda ke da kimanin mutum biliyan 1.3 a cikinta za ta samu sauki ganin cewa akwai kasashe da dama da ke ta kokarin kafa kamfanonin samar da rigakafi, akasari da taimakon sanannun kamfanonin kasa da kasa.
Kira a tashi tsaye
Karancin samar da rigakafi da Afirka take yi ya sa nahiyar ta samu gibi matuka ta fannin rigakafin a lokacin da ake ganiyar annobar korona.
Hakan ya tilasta wa kasashen nahiyar Afirka dogara kan irin rabo maras adalci da kasashen da suka ci gaba suke yi kan rigakafin.
Fiye da kashi 44 cikin 100 ne kacal na yan Afirka aka yi musu rigakafin korona haka kuma barazanar da koronar ke yi na kara karuwa, kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka ta bayyana.
An samu mace-mace fiye da 256,000 sakamakon annobar korona a nahiyar.
Amma baya ga cutar korona, Kungiyar Tarayyar Afirka ta kuma yi tunanin samar da rigakafi ga wasu cututtuka da suka hada da cutar Lassa da Zazzabin Rift Valley da Ebola da HIV da Kwalara.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce kasa da kamfanonin Afrika 10 da ke samar da rigakafi kuma kusan dukansu na a kasashe biyar ne da suka hada da Afirka Ta Kudu da Masar da Moroko da Senegal da Tunisiya.
Haka kuma kashi daya na rigakafin da ake amfani da su a nahiyar ne ake samar da su a Afirka.
Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka wato CDC na da burin ganin cewa kasashen Afirka sun samar da akalla kashai 60 cikin 100 na rigakafin da ake bukata, wato tsakanin rigakafi biliyan 1.4 zuwa biliyan 1.7 a duk shekara zuwa shekarar 2040.
“Sama da sababbin kamfanonin samar da rigakafi 30 ne ke kan hanya a Afirka, kuma ana ta kokari domin ganin cewa lamarin ya yiwu,” in ji Dakta Ahmed Ogwell, mukaddashin daraktan hukumar CDC
BionNTech ya soma gina kamfanin samar da rigakafinsa a Kigali a Yunin 2022.
“Ba wai Rwanda kadai kamfanin zai rinka samar wa rigakafi ba,” in ji Yvan Butera, karamin ministan lafiya na Rwanda. “Kamfanin zai rinka samar wa nahiyar.”
Kamfanin ya bayyana cewa sauran kamfanonin za su kasance a Senegal da Afrika ta Kudu.
A Kenya, Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta bayyana cewa ta kulla yarjejeniya da kamfanin Moderna na Amurka don soma gina kamfanin samar da rigakafinsa a watanni ukun farko na bana.
Kamfanin ya ce yana son samar da kimanin rigakafi miliyan 500 a duk shekara.
Hanya mai tsawo
Batun wadatar da kai ta hanyar samar da rigakafi lamari ne da zai dan dauki lokaci.
Binciken da Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta yi ya nuna cewa kasashe da dama na bukatar shirye-shirye na ilimi da ke da alaka da samar da rigakafi.
Akwai da dama da ke da ilimi wadanda suke tafiya yankunan da za a biya su kudade da kyau.
Rwanda da Kenya sun bukaci kamfanonin duniya da ke da burin kafa kamfanoni a kasashen su da su tabbatar sun horas da 'yan kasashen ilimin kimiyya.
Haka kuma hukumar ta CDC na bayar da kwarin gwiwa ga kasashe da su mayar da hankali kan abin da ya fi rigakafin.