Chilima ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarar 2014 / Hoto: AFP

Saulos Klaus Chilima, wanda aka haife shi ranar 12 ga watan Fabrairun 1973 a birnin Blantyre na Malawai, shi ne ɗa na farko ga Henderson Brown Chilima da Elizabeth Frances Chilima.

Ya taso a birnin Blantyre inda iyayensa suke aiki, suke kuma yawan zuwa ƙauyukan Lilongwe da Ntcheu inda kakanninsa suke zama a duk lokacin da ake hutu.

Ya auri Mary Nkhamanyachi Chilima wacce suka haifi 'ya'ya biyu da ita, Sean da Elizabeth.

Saulos Klaus Chilima ya auri Mary Chilima

Chilima ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Malawi a shekarar 1994, kana daga baya ya yi karatun digiri na biyu a jami'ar.

A shekarar 2015 ya kammala karatun digiri na uku a Jami'ar Bolton da ke Birtaniya.

Ya fara aiki a kamfanin Lever Brothers (Mw) Limited (wanda a yanzu ya koma Unilever) kafin daga baya ya koma kamfanin Leasing and Finance Company of Malawi, da kuma Southern Bottlers Limited.

Aikinsa na ƙarshe a kamfani shi ne wanda ya yi a kamfanin sadarwa na Airtel Malawi, inda ya jagoranci tawagar tallata kamfanin kafin daga bisani aka ba shi muƙamin babban daraktan kamfanin a shekarar 2010.

An rawaito cewa ya bunƙasa kuɗin shigar kamfanin na Airtel Malawi na shekara da kashi 75 cikin 100 a cikin shekara uku, daga dala miliyan 54 a 2010 zuwa dala miliyan 95 a 2013.

Harkokin siyasa

Chilima ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarar 2014, a lokacin da Shugaba Peter Mutharika ya ayyana shi a matsayin mataimakinsa a takara.

A lokacin yaƙin neman zaɓe a shekarar 2020 Malawi. Hoto: Saulos Chilima/X

Kazalika, ya bar tafiyar Mutharika a shekarar 2018 inda ya ƙaddamar da tasa jam'iyyar ta Transformation Movement (UTM) gabanin zaɓukan watan Mayun 2019.

A ƙoƙarinsa na samar da jamiyyar adawa mai ƙarfi, sai UTM ma Chilima ta kafa ƙawance da jam'iyyar Peoples Party ta Joyce Banda da jam'iyyar People's Movement ta Cassim ChilumphaTikonze da kuma wasu ƙananan jam'iyyun.

Sun amince su tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya, amma daga baya sai Joyce Banda da Cassim Chilumph suka janye daga ƙawancen, suna cewa ba su yarda da wanda aka tsayar a matsayin mataimakin ɗan takara ba.

Chilima ya samu kashi 20 cikin 100 na ƙuri'un a zaɓen wanda aka ayyana shugaban mai ci na lokacin eter Mutharika a matsayin wanda ya yi nasara.

Daga baya kotun kundin tsarin mulki ta Malawi ta soke zaɓen Mutharika, inda ta ce an lalata ƙuri'u, sannan aka sanya sabuwar ranar yin zagaye na biyu a watan Yunin 2020.

Saulos Chilima ya yi mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin Shugaba Peter Mutharika da Shugaba Lazarus Chakwera. Hoto: @Saulos Chilima/X

Lazarus Chakwera wanda ya zo na biyu a zaɓen, ya zaɓi Chilima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa. Da suka haɗa ƙarfi wajen ɗaya, sai da suka ture gwamnatin Mutharika da kashi 58 cikin 100.

Kazalika a shekarar 2022, Shugaba Chakwera ya raba Chilima da ikon da yake da shi a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa sakamakon badaƙalar cin hanci na dala miliyan 150, amma daga baya aka wanke shi daga tuhumar.

Chilima, ya rasu ne a kan hanyarsa ta wakiltar gwamnati a jana'izar Ministan Shari'a Ralph Kasambara, wanda ya mutu kwana uku kafin hatsarin.

Shugaba Lazarus Chakwera ya tabbatar da mutuwar Dr. Saulos Chilima da wasu mutum taran sakamakon hatsarin jirgin sama da ya faru a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni. /Hoto: @Saulos Chilima/X
TRT Afrika