Djado na nan a yankin Kawar na sahara mai nisan kilomita 1,300 daga Yamai Babban Birnin Nijar, kuma kusa da iyakar Nijar da Libiya da ake rikici a cikin ta. / Hoto: AFP

Takakkiyar tafiya a saharar arewa maso-gabashin Nijar na kai maziyarta ga daya daga cikin wuraren ban mamaki a yankin Sahel: kauyukan da aka yi wa yabe da ruwan gishiri da tabo, sannan kuma suke tsaye a kan garin yashin sahara.

Matafiya a zamani daban-daban na tsayawa a kusa da “gidajen” da ke Djado, suna mamakin irin katangun gidajen da hasumiyoyi da hanyoyin boye da rijiyoyi, dukkan suna nuna kwarewar gine-ginen da ba a san wadanda suka yi su ba.

Su wane ne suka zabi gina wannan waje a tsakiyar sahara da zafin rana kuma a yankin da babu kowa – kuma me ya sa suka gina su? Wadannan ne tambayoyin da ba a taba bayar da cikakkiyar amsarsu ba. Kuma abin rikitarwa shi ne, me ya sa aka yi watsi da gine-ginen?

Babu wani bincike na tarihin zamantakewar jama’a ko na kimiyya da aka taba yi da ya fayyace wannan waje mai ban ta’ajibi.

Yankin Kawar da a baya ya zama hanyar fatake da ke kasuwanci a yankunan sahara, a yanzu ya zama matattarar fataucin makamai da miyagun kwayoyi/ Hoto: AFP

Djado na nan a yankin Kawar na sahara mai nisan kilomita 1,300 daga Yamai babban birnin Nijar, kuma kusa da iyakar kasar da Libiya.

Yankin Kawar da a baya ya zama hanyar fatake da ke kasuwanci a yankunan sahara, a yanzu ya zama matattarar fataucin makamai da miyagun kwayoyi.

Munin yanayin da yake ciki ne ke razanar da fatake.

“Tun shekarar 2002 babu dan yawon bude ido na kasar waje da ya zo nan”, in ji Sidi Abba Laoel, magajin Chirfa, garin da ke yankin na Djado.

“A lokacin da ake samun masu yawon bude ido, akwai bunkasar tattalin arziki ga jama’ar yankin”.

A 2014 an gano zinare a yankin kuma daga nan ne aka rika samun kwararar masu hakar ma’adanai daga Yammacin Afirka. Hakan ya farfado da rayuwa da bunkasar tattalin arziki ga jama’ar, amma kuma akwai ‘yan bindiga da ke addabar yankin.

Munanan hare-hare

Magajin garin yana kula sosai wajen bayanin tarihin yankin, inda yake bayyana gibin ilimi da aka yi ta samu kan wannan wuri.

Yana duba kwafin takardun da Albert le Rouvreur, wani jami’in sojin ‘yan mulkin mallakar Faransa, ya rubuta. Albert ya yi kokarin karin hake game da wajen, duk da dai shi ma bai yi nasara ba.

A tsakanin karni na 13 da 15, jama’ar Kanuri sun kafa kansu a yankin/ Hoto: AFP

Al’ummar Sao da ke zaune a yankin tun tale-tale, su ne aka sani da fara zama a Kawar, kuma suka fara yin gini a yankin.

Amma babu tabbacin lokacin da suka tare a wajen. Wasu daga cikin dakunan da ke tsaye har yanzu na da rufin ciyayi, hakan na nufin daga baya aka gina su.

A tsakanin karni na 13 da 15, al'ummar Kanuri sun kafa kansu a yankin.

A karni na 18 da na 19 sai da aka kusa gamawa da alamunsu saboda hare-haren makiyaya – Tuareg, Larabawa da Toubou.

Sakamakon fara zuwan Turawa yankin a karni na 20 ne ya kawo karshen gidajen a matsayin wajen kariya daga mahara. A 1923 ne sojojin Faransa suka kwace iko da yankin.

A yau Kanuri da Toubou sun cakudu da juna sosai amma shugabannin yankin na kiran cewa ‘Mai’ na daga tsatson Kanuri.

Sun zama kamar masu kula da wadannan kaya kuma masu kare tarihi a baki.

“Ko kakanninmu ma ba su san tarihin wurin nan ba. Ba mu ajiye wasu bayanai kan wurin nan ba,” in ji Kiari Kelaoui Abari Chegou, wani shugaban jama’ar Kanuri.

Tun 2006, Djado ya zama a jerin sunayen wuraren tarihi na UNESCO/ Hoto: AFP

Labaran tasirin Turkawa

A nisan kilomita 300 kudu da Djado akwai saharar Fachi, wadda ta shahara da tsohon garin da ake da shi, inda har yanzu katangunsa suke tsaye kyam.

Har yanzu ana amfani da alamun garin a yayin bukukuwa.

Wani shugaban gargajiya a Fachi, Kiari Sidi Tchagam, ya ce wannan tsohon garin ya fi shekaru dari biyu.

“A bayanan da muka samu, akwai wani Balarabe wanda ya zo daga Turkiyya, shi ne ya bai wa mutanen wajen shawarar gina gari a nan," ya fada yana bayar da bayani kan Turkawa.

A yayin da mutane ke alfahari da wajen, an kuma nuna damuwa game da rashin kwarin wajen da aka gina da gishiri, wanda ruwan sama ke wa barazana matukar ba a kula da shi ba.

Tun 2006, Djado ya shiga jerin sunayen wuraren tarihi na UNESCO.

“Yana da matukar muhimmanci sanya shi a jerin wuraren tarihi,” in ji Tchagam.

Ya ce “Wannan waje na tunatar da mu kawunanmu sosai, wani bangare ne na al’adunmu da tarihinmu baki daya.”

AFP