Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce za ta soma yi wa ganuwar da ta zagaye birnin na Kano kwaskwarima da zummar "dawo da kyawunta".
"A yunkurin da ake yi na dawo da kyawun ganuwar Kano kamar yadda hukumar kula da kayan tarihi ta kasa ta ayyana ta a matsayin wurin tarihi, gwamnatin Kano ta tsara yin kwaskwarima ga ganuwar da ke tsohon birnin Kano ta hanyar amfani da baraguzan gine-ginen da aka rusa kwanan nan a birnin," in ji sanarwar da gwamnatin ta fitar a yau Litinin.
Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki wurin ganuwar da aka rusa, a cewar kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Ya kara da cewa za a amfani da "baraguzan gine-ginen da aka rusa kwanan nan a birnin wajen sake gina ta, kuma ba a bukatar mutanen da ba su da nasaba da aikin rusau din da ake yi halartar wuraren.
"Sannan an bai wa 'yan sanda da jami'an hukumar taro ta Civil Civil Defence Corps (NSCDC) umarnin zuwa wurin domin kare shi daga masu kutse".
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce hukumomi za su dauki mataki kan duk wani "mai kunnen-kashi" da aka gan shi a wuraren.
Masana tarihi sun ce an kwashe dubban shekaru da gina ganuwar Kano.
Tun bayan shan rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soma rusa wuraren da ya ce gwamnatin da ta gabata ta gina ba bisa ka'ida ba,
Lamarin ya jawo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke goyon bayansa yayin da wasu ke yin tir da shi.
Gwamnan ya zargi gwamnatin mutumin da ya gada, Abdullahi Umar Ganduje, da sayar da filaye da bayar da umarnin gine-gine ba bisa ka'ida ba, ciki har da filayen makarantun gwamnati, asibitoci, makabartu da sauransu.
Sai dai tsohon Gwamna Ganduje ya sha musanta cewa ya aikata ba daidai ba, yana mai karawa da cewa Gwamna Yusuf bai san aikinsa ba.