An rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban Nijeriya a ranar Litinin.
A makon da ya wuce ne Kashim Shettima da iyalansa suka dauki hankalin 'yan Nijeriya bayan da aka ga hotunansu a yayin da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari yake bai wa sabon mataimakin shugaban kasar lambar girma ta GCON.
Hotunan na nuna Shettima da matarsa Hajiya Nana da wasu 'ya'yansa biyu mace da namiji, "cikin kwarjini da kamala", kamar yadda mutane suka yi ta tsokaci.
Sanata Shettima, mai shekara 56, ya yi gwamnan Jihar Borno tsawon shekara takwas tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, inda daga nan ya zama dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar tsakiyar Jihar Borno.
Ya yi digiri a fannin tsimi da tanadi a aikin gona (Agricultural Economics) daga Jami'ar Maiduguri a shekarar 1989, kuma ya yi aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Cross Rivers.
Daga bisani ya yi digirinsa na biyu a Jami'ar Ibadan da ke kudu maso yammacin Nijeriya har ila yau a fannin tsimi da tanadi a aikin gona a shekarar 1991.
Ya taba koyarwa a Jami'ar Maiduguri tsakanin shekarar 1991 zuwa 1993. Daga bisani kuma ya koma aikin banki a jihar Legas, inda ya yi aiki a bankuna daban-daban ciki har da bankin Commercial Bank of Africa Limited da kuma Zanith Bank.
Sabon mataimakin shugaban Nijeriya ya rike mukamin kwamishina a ma'aikatu da dama a jihar Borno tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011.
Ko da yake matarsa daya, duka iyayen Shettima sun rasu.
Ya auri matarsa Nana Usman Alkali a shekarar 1988 wato shekara 35 da suka wuce kenan.
Ita ma ta yi karatunta ne a Jami'ar Maiduguri, inda ta yi digiri a harshen Turanci da Adabi.
Nana, mai shekara 47, wacce aka haifa a Jihar Kano kuma Allah Ya albarkace su da 'yaya uku ciki har da Fatima wadda ta auri dan gidan tsohon Ministan Abuja Arc Ibrahim Bunu, Sadiq, a bara.