Wata bishiyar auduga mai dimbin tarihi a Saliyo ta fadi bayan tsawon shekaru, a Freetown babban birnin kasar.
Mamakon ruwan sama a ranar Larabar da ta gabata ne ya fado da bishiyar, in ji Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio.
Da yake bayyana wannan abu a matsayin babbar asara ga kasar, Bio ya ce "Ita (Bishiyar Audugar) ta zama wata alama ta 'yanci da walwalar jama'ar da suka fara riskar ta.”
Ya kara da cewa "Za mu samar da wani abu a wannan waje da zai zama shaidar wannan Bishiya ta Auduga mai girma da ke da matsayi a tarihinmu. Za a saurari dukkan ra'ayoyi game da wannan.”
Wani sanannen jarumin fim Idris Elba, dan kasar Ingila da ya samo asali daga Saliyo ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa "Wannan (faduwar bishiyar mai daraja) abin bakin ciki ne. Jijiyar za ta kasance a Saliyo".
Mahaifin jarumin da aka haifa a Landan, Winston Elba dan kasar Saliyo ne da ke Afirka.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin da bishiyar ta fadi kasa, wanda hakan ya sanya mutanen da ke kewayen suka cika da alhini da bacin rai.
Yvonne Aki-Sawyerr, tsohuwar shugabar birnin Freetown ta ce ta ji "Tsananin rashi da tafka asara" bayan samun labarin faduwar bishiyar.
A sanarwar da ta fitar ta ce "Bishiyar audugar ita ce tsakiyar birninmu ta hanyoyi daban-daban, kuma wani bangare na tarihinmu baki daya."
Bayanan da aka samu a tarihi sun yi nuni da cewa bishiyar ta fara yin shuhura a shekarar 1792 lokacin da wasu mutane da aka bautar suka koma Freetown da zama.
Tsofaffin bayin sun kai kusan su 4,000. Bayan iyayen gidansu na Birtaniya sun 'yanta su sakamakon juyin juya halin Amurka, sai aka jibge su a Saliyo ba tare da duba da asalin kasashen da suka fito ba..
A shekarar 1791 wasu mutane a jirgin ruwa daga Nova Scotia, Kanada suka zo gabar tekun Saliyo, kuma suka tafi wajen wannan katuwar bishiya ta auduga inda suka yi addu'o'i da wakokin ibada a wajen.
Daga baya bishiyar ta zama alamar yalwar tarihi da kayan da aka gada masu daraja.
Duk da ba a san takamaiman yawan shekarun bishiyar ba, amma an bayyana cewa ta wanzu tun 1787, wato tana da shekara kusan 236, inda rayuwarta ta kawo karshe a ranar Laraba 24 ga Mayu, 2023.
Bishiyar ta auduga ta zama wata babbar alama a babban birnin Saliyo na Freetown, kuma an saka hotonta a jikin takardar kudin kasar ta Leones 10,000.