Jirgin ruwan Maroko na yaki Es Sid El Turki, 1894. Hoto/Arab Defense Forum

Daga Seddiq Abou El Hassan

A lokacin da nake kallon wata bitar tarihi da wani mai wallafa bidiyo a YouTube na kasar Amurka yake yi, sai na yi matukar sha’awar sunan wani jirgin ruwa na yaki wanda sojojin ruwa na Maroko suka saya na zamani.

Sid El Turki wani suna ne na musamman ga jirgi na biyu na zamani wanda aka yi amfani da shi a rundunar sojin ruwa ta Maroko a shekarun karshen karni na 19, wanda wani karin jirgi ne wanda aka gina shi asali domin daukar kaya wanda wani kamfanin kera jiragen ruwa na Jamus Bremen ya kera shi.

An sayar wa Maroko da shi inda aka mayar da shi jirgin yaki da kuma shawagi, an kuma yi amfani da jirgin a lokacin yakin Sifaniya da Maroko na karshe a karshen shekarun 1890 da kuma farkon 1900.

Jirgin wanda yake daukar akalla mutum 100, kuma yake dauke da manyan bindigogi masu tsawon millimeter 76 kirar Birtaniya, Sid El Turki ya yi amfani matuka a matsayin jirgi na yaki da kuma jigilar dakarun soji a cikin ruwa, a lokacin da Sifaniya da Faransa suka mamaye Maroko a hankali.

A ranar 4 ga watan Fabrairun 1938, jirgin Sid El Turki ya nutse sakamakon guguwar teku, lamarin da ya kawo karshen wannan jirgin yakin wanda ya shafe shekaru 40 yana aiki ba kakkautawa.

Tarihi a takaice

Kasashen Turai na ta son mamaye wani yankin Larabawa daga bangaren Afirka tun karni na 11.

Jiragen ruwan mutanen Norman, wadanda na yan kasuwa ne, ‘yan kasar Portugal da Sifaniya sun kara habaka a lokacin da Daular Almohad ta kara rauni, inda kuma daulolin da suka biyo baya suka shiga rudani da halaka.

Daya bayan daya, kasashen da suke da teku daga Tripolitania zuwa Ceuta sun fada hannun sarakunan Turai masu tasowa, ta hanyar yake-yaken soji da suka kaddamar ba kakkautawa wanda Coci ta bayar da goyon baya da kuma samun tallafi daga sarakunan Kiristanci na Katolika.

Duk da juriya irin ta jarumta, rashin daidaita a karfin makamai ya ba wa daular Portugal damar ƙwace manyan tashoshin teku masu yawa da ke kan tekun Atlantika.

Daga wuraren da suka mamaye, ba da jimawa ba sojojin Portugal suka ci gaba faɗaɗa yankuna kuma suka fara mulkin mallaka wadda wani lamari ne mai daci idan an tuna nasarar da suka samu ta yakin Castile da Aragon na al-Andalus.

A shekarar 1578, sojojin Saadi karkashin jagorancin Abd al-Malik da dan uwansa Ahmad al-Mansour suka kawo karshen fadada yankunan da Portugal ke yi a Maroko a yakin Wadi al-Makhazin (wanda aka fi sani da yakin sarakuna uku).

Wannan yakin ya yi tasiri matuka kan duka bangarorin da ke mashigar ruwa ta Gibraltar, inda kuma ya taka rawa wurin mayar da ikon mulki ga Maroko har zuwa lokacin da sarakunan kasar suke iko da kabilun da ke ba su ciwon kai.

Sannan a daidai lokacin da karfin iko ya soma rauni, kasar sai ta kara shiga wani hali na daukaka da kuma rushewa.

Daukaka da kuma rushewa

Tun daga farkonta, kaddarar Daular Saadi na tattare da habakar Daular Usmaniyya. Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa wata rundunar sojojin Daular Usmaniyya karkashin jagorancin Abd al-Malik da kansa na da zuciyar magance matsalolin da ake da su kan batun wanda zai gaji sarauta a Daular Saadi, inda ya kafa daula mai karfi wadda za ta mayar da hankali wurin ‘yanta biranen da ke gefen teku wadanda aka mamaye.

A zahiri, Sarakunan Daular Saadi sun rinka amfani da tsarin soji na Daular Usmaniyya inda suka yi kokarin kwaikwayon yanayin rundunoninsu da mukamai da bukukuwa da tufafinsu.

Sakamakon da aka samu na yakin Wad al-Makhazin ya kara karfafa gwiwar sojojin Saadi domin su goyi bayan tsarin Usmaniyya, wanda ya kawo karshen dogara da tsarin yaki na gargajiya wanda ake amfani da dawakai a kai hari sannan a ja da baya.

A karkashin Ahmad al-Mansur, musamman sojojin Maroko sai suka zama cikin tsari inda aka rarraba masu mukamai daban-daban. Akwai mukamai na Turkiyya da suka hada da sipahi da beylerbey da suka kawo.

A karkashin Daular Alawi, Sultan Mohammed III ya gayyaci kwararru daga Santambul, wato birnin Daular Usmaniyya domin farfado da kamfanin hada makamansa wanda ke cikin wani hali Masanin tarihi Abdelhaq Elmarini ya bayar da bayanai a littafinsa al-jaysh al-maghribi abr at-tarikh ( Sojojin Maroko a tarihi): “ A 1767, an tura wasu kwararru 30 daga Daular Usmaniyya zuwa Marako inda kuma aka rarraba su zuwa gida hudu, bisa kwarewarsu: masu kera jirgin ruwa, masu hada bamabamai, da masu hada igwa da wadanda suka shahara wurin harba bam mai masakin tabarya.

Sai sarkin ya bayar da masu kera jiragen ruwa ga tashar ruwa ta jihadiya wadanda ke bakunan teku biyu (akasari biranen Rabat da Sale da ke dayan bangaren kogin Bou regreg).

Sai suka zama daya daga cikin makaman Rabat, tare da masu sana’o’in Maroko. Wasu daga cikin injiniyoyi Turkawa sai suka kafa kansu a Fez inda suka sadaukar da kansu da su koya wa ‘yan Maroko kwarewar da suke da ita, a sabon makamin atilarin da suka kera.

Wasu ruwayoyi kuma sun bayyana cewa Mohammed III wanda ake cewa shi ne ya kirkiro sabuwar Maroko, shi ya assasa wuraren ayyukan karfe da wasu ayyuka masu dogon buri.

Bugu da kari batun da ake yi na “kwararrun da aka dauko daga Astana” tare da sauran yankuna a wurare da dama an nuna cewa a lokacin mulkinsa ne, duk a yunkurinsa na habaka daular domin ta yi gogayya da Turai.

Wannan sarki ya yi watsi da abin da ake gani na assha ne lokacin da ya umarci wani masanin gine-gine na Faransa da gina Essaouira, babban birninsa, kan tsohon Tsibirin Mogador.

Daukaka da yabawa

Sakamakon haka ne Mohammed III ya gina wani babban kamfanin hada bama-bamai a Tetuan karkashin sa ido na kwararrun Turkiyya wadanda suka koya wa ma’aikatan Maroko aikin hada bama-bamai.

Manya-manyan harsasan da aka kera a kamfanonin da su aka yi amfani aka fasa bangon Mazagan domin ‘yanta kansu daga Portugal.

Duk da cewa ba a samu bayanai kan kwararrun Turkiyya da suka je can ba sakamakon baki daya sun hade da mutanen Maroko, amma sunaye biyu sun tsira a rukunin na ƙarshe.

Masu aikin fasaha biyu wadanda suke da sunan mahaifi daya Eldrizi (wanda ke wakiltar sunan mahaifi a Algeria da Libiya), haka kuma watakila an saba sunan Albaniya ne na Idrizi.

Ismail Eldrizi da Suleyman Baba Eldrizi, haka kuma an san shi da sunan Hajj Suleyman Bombaci, wanda sunansa ya kare da karin Turkiyya na “–ci” wanda yake karin bayani kan aikin da yake yi, inda haka lamarin yake ga iyalai da dama da ke Arewacin Afirka wadanda asalinsu daga Daular Usmaniyya suka fito.

Sadaukar da kai da kuma kirkire-kirkiren da yake yi sun sa ana daraja shi a tsakanin ‘yan Maroko.

Dakarun da ke cikin Es Sid El Turki, 1894. Hoto/Arab Defense Forum

A littafinsa na Tarikh al Du’ayyif, masanin tarihin ya rubuta cewa: “Shi ne [Hajj Suleyman] wanda ya koya wa ‘ya’yan Rabat da Sale [harbin bindiga].” Masanin tarihin kuma masanin kasa Abu al-Qasim al-Zayani (1734/35-1833) watakila yana batu ne kan Hajj Suleyman El Turki a lokacin da ya bayyana cewa “yana koya wa ‘yan Sale da Rabat harbin bindiga, inda da dama daga cikinsu suka zama kwararru wurin harbi.

Shi dai wannan masanin tarihin ya sake yin magana a kan Hajj Suleyman El Turki a lokacin da ya bayyana irin muhimmiyar gudunmawar da ya bayar a lokacin da aka mamaye El-Jadida.

Shi ya sa shaharar da ya yi ta fi rayuwar da ya yi. Ana ganin sakamakon irin darajarsa ne Sultan Hassan I ya bai wa daya daga cikin jiragen ruwan yakin Morocco na farko kuma na zamani sunansa.

TRT Afrika